✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambode Ya yi juyayin rashin babban limamin Legas

Allah Ya yi wa babban limamin Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Garba Akinola rasuwa. Kafin rasuwar tasa, shi ne limamin babban masallacin da ke tsakiyar garin…

Allah Ya yi wa babban limamin Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Garba Akinola rasuwa. Kafin rasuwar tasa, shi ne limamin babban masallacin da ke tsakiyar garin Legas.

Shekh Ibrahim ya rasu yana da shekaru 79 a ranar Lahadin da ta gabata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar jinya. An kuma yi masa sutura a ranar Litinin ɗin da ta gabata kamar yadda Musulunci ya tanada.

Shaihin malamin ya yi karatun addini a fitacciyar makarantar nan ta Markaz da ke Agege Legas a shekarun 1956 zuwa 1961, ya zama babban limamin Legas yana da shekaru 63. Kafin nan ma’aikaci ne shi, inda ya yi aiki na tsawon shekara 32, bayan ya yi ritaya sai ya ci gaba da limanci.

Marigayin ya samu kyakkyawan yabo daga al’ummar Jihar Legas. daya daga cikin muƙarrabbansa kuma hadimi a masallacin na tsakiyar birnin Legas, Malam Abdurashid Umar Ambasadan kadiriyya, ya shaida wa Aminiya cewa sun sami kyakkyawar tarbiya daga shaihin malamin. Ya ce a duk lokacin da ya yi magana da shaihin malamin sai ya sa shi zubar da hawaye, domin yakan ce shi mutuƙar yana raye to ba ya so ya ji hankalin wani mahaluƙi ya tashi.

Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode ya bayyana shaihin malamin a matsayin mutum nagari, mai tsage gaskiya, wanda jama’ar jihar za su daɗe suna kewarsa.