✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta yi barna a sansanin ’yan gudun hijira a Borno

Mamakon ruwan saman ya yi sanadin rasa matsuguni ga 'yan gudun jihar.

Dubban ’yan gudun hijira da ke zaune a sansanin Bakassi na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun rasa matsuguni sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a yammacin ranar Talata.

Rahotanni sun ce an tafka ruwan saman kamar da bakin kwarya wanda ya sauka a Yammacin ranar Talata.

  1. Kwalara ta yi ajalin mutum 75 a Katsina
  2. Kwamandojin Boko Haram na neman yafiyar ’yan Najeriya

Mamakon ruwan saman wanda a janyo ambaliya ya rutsa da kimanin ’yan gudun hijira 6,830 daga Marte, Guzamala, Gwoza, Monguno da sauran al’ummar Kananan Hukumomin da ke zaune a sansanin na Bakassi.

Ambaliyar ta jefa mutane cikin tsaka mai wuya la’akari da yadda ’yan gudun hijirar suka rasa matsuguni duk da fargabar barkewar cutar kwalara.

Wakilinmu da ya ziyarci sansanin da safiyar ranar Laraba, ya gano cewar ambaliyar ta mamaye dukkan tantuna da sauran ofisoshi da kungiyoyin agaji suka gina.

Bura Kaka, daya daga cikin ’yan gudun hijirar ya yi kira ga gwamnati da sauran kungiyoyi da su samar musu da matsuguni da ya dace a Bakassi.

“Ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya sauka a jiya (Talata) da misalin karfe 4:50 na yamma, ya janyo ambaliyar da ta sanya yadda muka ga rana haka muka ga dare, musamman wasu daga cikin mu da ke zaune a cikin tantunan da ba su dace ba.

“Duk sansanin ya cika da ruwa. Muna bukatar taimakon gaggawa daga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu domin har yanzu ruwan saman na ci gaba da sauka.

“Akwai bukatar masu hannu da shuni da gwamnatin jihar su duba wannan mummunan halin da ake ciki da kuma bullar cututtukan da ke barkewa kamar amai da gudawa da zazzabin cizon sauro, macizai da sauransu,” in ji Kaka.

A yayin da lamarin ya faru, wani jami’in Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ya shaida wa wakilinmu cewa hukumar tare da hadin gwiwar Hukumar SEMA ta jihar na aiki tukuru don samar wa da wanda abin ya shafa mafita.

“Mun gudanar da aikin tantancewa tare da hadin gwiwar SEMA a sansanin ’yan gudun hijira na Bakassi don haka mun nemi SEMA da ta dauki matakin da ya dace kuma muna da yakinin tuni sun fara aiki kamar yadda aka tsara,” a cewar jami’in NEMA.