✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 a Binuwai

Akalla mutum 116,084 sun rasa muhallansu.

Daga farkon daminar bana kawo yanzu, an samu akalla mutum 23 da suka rasa rayuwakansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Binuwai. 

Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na jihar, Dokta Emmanuel Shior ne ya bayyana haka rana Talata a Makurdi, babban birnin jihar.

Ya yi bayanin ne a wajen taron kaddamar da shirin raba kayyakin tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa a fadin jihar.

Ya ce aukuwar ambaliyar a wasu sassan jihar ya sa akalla mutum 116,084 sun rasa muhallansu da lalata dimbin dukiya, gidaje masu yawa da gonaki da sauransu.

Shior ya kara da cewa, mutum 116,084 da ibtila’in ya shafa sun fito ne daga gidaje 12,856 kuma a tsakanin kananan hukumomi 11.

“Mutum 74 daga ciki sun ji raunuka daban-daban, sannan 14 daga cikin mutum 23 da suka mutu sun cim ma ajali ne sakamakon kifewar jirgin ruwa,” inji shi.

A cewar Sakataren, kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa sun hada da Guma da Vandeikya da Otukpo da Katsina-ala da Makurdi da Apa da Agatu da Tarka da Gboko da Gwer ta Yamma da kuma Logo.

(NAN)