Ambaliyar ruwa ta datse babbar hanyar Bauchi zuwa Gombe, lamarin da ya bar masu ababen hawa suka yi curko-curko.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce daya daga cikin manyan kwalbatin da ruwa ke bi ta datse sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a kwanakin nan.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu cikin kasa mako uku da ambaliyar ruwa ke hana matafiya wucewa ta hanyar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, ya ce a yanzu matafiyan da suka taso daga Adamawa zuwa Abuja, sai dai su bi hanyar Gombe zuwa Dukku Darazo zuwa Bauchi da kuma Jos zuwa Abuja.
A halin yanzu an tura jami’an tsaro kan hanyar don tabbatar da kubutar ababen hawa, da kuma kiyaye salwantar rayuka ko dukiyoyin al’umma.