✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar Ruwa: Peter Obi ya raba burodi 24 a matsayin tallafi

Bashir Ahmad ya yi martani kan sakon da Peter Obi ya wallafa.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya mika wasu ‘yan kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Anambra

Cikin kayan da dan takarar ya aika har da wasu ‘yan kwayoyin burodi 24 wanda kuma ya saka a shafinsa na Tuwita.

Ya mika kayayyakin ne ga wasu mazauna Ogbaru wadanda ke zaman gudun hijira a wani sansani a garin Atani na jihar.

Ganin ‘yan kayayyakin, Bashir Ahmad mai ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokoin sadarwa na zamani ya nuna kaico, la’akari da matsayin dan takarar.

Hadimin Shugaban Kasar ya yi martani kan sakon da Peter Obi ya wallafa yana mai bayyana mamakin yadda Gwamnatin Tarayya ba ta ayyana dokar ta baci ba yankin da hakan zai sa ta samu taimakon gaggawa.

Hakan ta sa mutane daban-daban, musamman daga yankin, suka mayar da martani  kan kalaman na Bashir, inda wasu ke ganin bai kyauta ba shi da Shugaba Buhari.

Cikin kayan da Peter Obi ya aika da su a matsayin tallafi da akwai buhun shinkafa, taliyar yara, da barguna, da injin markade da kuma injin janareta karami.

%d bloggers like this: