✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa: Mutane sun koka da halin ko in kula

Wanda ambaliyar ruwa ta afkawa a jihar Jigawa sun koka game da irin halin da suke ciki.

Daruruwan mutane da ambaliyar ta shafa a karamar hukumar Hadeja da ke jihar Jigawa sun koka da mummunan halin da suke ciki a sansanin agaji.

Wadanda ambaliyar ta shafa da ke zaune a sansanin agaji 13 a Hadejia,  sun koka da yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su tare da barinsu cikin mawuyacin hali.

A wata sanarwa da shugabar gidauniyar mata da marayu da marasa galihu a Hadeja Malama Fatima Kaila ta fitar, ta ce gwamnatin Jigawa ba ta nuna kula wa ba tun lokacin da mummunan bala’in ya kori wadanda ambaliyar ta fatattaka daga gidajensu.

Ta roki gwamnati da masu ruwa da tsaki da ke jihar da su taimaka wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama na guduwa daga sansanonin ‘yan agajin saboda sau daya suke samun abin da zasu ci a rana.

A wannan shekarar an samu ruwan sama mai yawan gaske da ya yi sanadiyyar lalata gidaje da gonakin mutane da dama a jihohin Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi da sauransu.

Sai dai tun bayan aukuwar ambaliyar ruwan, shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa da ta yi bincike tare da ba da agaji ga wanda abun ya shafa.