✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa: Buhari ya bayar da umarni fitar da Tan 12,000 na hatsi

Shugaba Buhari ya bayar umarnin a fitar tan 12,000 na hatsi ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta shafa.

Shugaba Buhari ya bayar umarnin a fitar tan 12,000 na hatsi ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta shafa.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) Mustapha Habib Ahmed ne ya bayyana haka a Abuja a yayin bikin ranar agaji da kuma rage radadin bala’o’i ta duniya.

Buhari ya bayar da umarnin fito da hatsin ne daga rumbun ajiyar hatsi na Gwamnatin Tarayya.

Shugaban Hukumar NEMA ya ce, suna iya bakin kokarinsu na aikawa da kayyakin agajin gaggawa ga wadanda ambaliyar ruwan ta shafa kamar yadda ta saba.

Sannan ya ce, duk da cewa ambaliyar ruwar da ake fama da shi a Lakwaja na hana safarar kayayyakin agajin, hukumarsa na aiki da hukumomin tsaro don tabbatar da an wuce da kayyakin lafiya.