Mutum shida ’yan gida daya sun mutu bayan gini gidansu ya fada a kansu a sakamakon amabliyar ruwa a Jihar Kebbi.
Ginin ya fada a kan wani magidanci da matarsa da ’ya’yansu hudu ne bayan kwana ruwan sama mai karfi na kusan awa biyu da aka yi da tsakar daren Litinin.
- Yadda ambaliya ke neman kawo karancin abinci a Najeriya
- Ambaliya ta yi kisa tare da lalata amfanin gona na Naira biliyan biyar a Kebbi
- Ambaliya ta kashe mutum 4 ta rusa gidaje 5,200 a Kano
Wani mazaunin garin Lauwali Yaldu ya ce da babban dan magidancin shi ne kadai ya tsira, kasancewa yaron yana makaranta a lokacin da abin ya faru.
Lauwali Yaldu ya ce Iftila’in wanda ya ruwa wasu gidaje a garin, ya faru ne a lokacinda ba za ka iya kai wa iyalan dauki ba, a garin Tungar Gyado da ke Kauyen Kwanawa a Kasar Yeldu, Karamar Hukumar Arewa ta Jihar.
Tuni dai aka yi jana’izar mamatan aka kai su makwancinsu kamar yadda addinin Islama ya tanada.
Mutuwar iyalan da aka yi jana’izarsu a ranar Litinin ta jefa garin cikin juyayi a Jihar da ke fama da matsanancinyar ambaliya tare da jawo dimbin asara.
A rahotannin Aminiya na baya ta ruwaita ambaliya ta lalata amfanin gona da aka kiyasata sun kai Naira biliyan biyar, baya ga gidaje da asarar rayuka.
Ko a ranar Lahadi rahotanni sun nuna ambaliyar ruwan sama ta yi barna sosai a garin Argungu da ke jihar.