Ambaliyar ruwa ta yi sanadin rasa rayukan mutum uku, tare da lalata gidaje da gonaki na biliyoyin Naira a Jihar Bauchi.
Hakan ya faru ne sakamakon shafe kwanaki uku da aka yi ana mamakon ruwan sama a ƙananan hukumomi uku na jihar.
Babban Daraktan Hukumar Bayaf da Agajin Gaggawa na Jihar (SEMA), Mas’ud Aliyu ne, ya tabbatar da hakan a ziyarar da ayarin da Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Ibrahim Kashim ya kai wa unguwannin da abin ya shafa.
Aliyu, ya ƙara da cewa, ambaliyar ta raba dubban mutane da muhallinsu da dabbobi da gonaki da suka lalace.
Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa sun haɗa da Katagum, Shira da Giade.
Ya ƙara da cewa hanyar Azare zuwa Isawa ta ɓalle, inda jama’ar unguwanni da dama suka maƙale.
Ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati za ta tallafa musu domin rage raɗaɗin asarar da suka yi.
Kwamitin, ya ziyarci ƙaramar hukumar Giade ne, domin tantance irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.
Ayarin ya kuma duba hanyar Giade zuwa Azare da Azare zuwa Jama’are mai titi biyu na babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri wadda ita ma ta rufta.
Har wa yau, kwamitin ya kuma gabatar da kayayyakin agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin ƙananan hukumomi uku.
Kazalika, kamfanin gine-gine na MotherCat Construction Limited ya ƙudira aniyar gyara ɓangaren ɗaya na hanyar Kano zuwa Maiduguri da ya lalace.