✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Fursunan da ya tsere ya shiga hannu a Maiduguri 

Fursunan ya shiga hannun jami'an tsaro ne biyo bayan wasu bayanai da suka samu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta yi nasarar sake cafke ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere a birnin Maiduguri na Jihar Borno, biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku.

Fursunan mai suna, Abubakar Mohammed, mai shekara 27, wanda tsere daga gidan yari a Maiduguri, biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku.

A ranar 15 ga watan Satumba, 2024, da misalin ƙarfe 3 na rana, wani mazaunin unguwar Bulakara da ke ƙaramar hukumar Gubio, ya sanar wa ‘yan sanda rahoto game da ganin fursunan.

Majiyar ’yan sanda ta ruwaito cewar, jin wannan rahoto ke da wuya ta tawaga ta musamman wadda ta samun nasarar cafke shi.

Rundunar ta ce za ta miƙa Abubakar ga hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya.

Har wa yau, ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo ragowar da suka tsere.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron jama’a.

Kazalika, ta yi kira ga jama’a da su bayar da bayanai kan duk wani abu da suke zargi a a yankunansu domin tallafa wa ƙoƙarin ‘yan sanda.