✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Al’amura sun munana a Borno — SEMA

Hukumar ta ce yanzu haka jami'anta sun maƙale a wajen ceto mutane.

Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Malam Barkindo Mohammed, ya bayyana cewar halin da ake ciki a Maiduguri sakamakon afkuwar ambaliyar ruwa ya munana.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito Dam ɗin Alau ne ya ɓalle da sanyin safiyar Talata, lamarin da ya sa ruwa ya mamaye yankuna da dama a garin.

Dubban mazauna garin sun rasa matsugunansu kuma suna neman wuraren da za su fake.

Mohammed, ya ce hukumar ta fara aikin ceto da kuma raba buhunan yashi don hana ruwan ya ƙara kwarara zuwa wasu yankuna.

“Muna kan aikin ceto yanzu haka, kuma mun raba buhunan yashi a Gozari. Yayin da nake magana da ku yanzu, ni da ma’aikatana mun maƙale; mun zo ceton wasu mutane amma yanzu muna cikin tsaka mai wuya,” in ji shi.

A halin yanzu, ɗaruruwan mutane sun nemi mafaka a kan tituna ba tare da sanin inda za su je.

Wasu mazauna garin na zaune ko kwance ne a ƙarƙashin bishiyoyi tare da iyalansu.

Wani magidanci mai mata biyu da yara shida, Musa Abbas, ya ce ba shi da inda zai je.

Ya ce ’yan uwansa suna zaune a yankin Bulumkutu, amma ya ce kafin zuwa wajensu dole ne a haye wata gada wadda ruwa ya shanye

“Yanzu gadar ta nutse a cikin ruwa; ba zan iya hayewa ba sai dai ‘yan uwana su zo su ɗauke ni. A nan za mu kwana, kuma za mu ci gaba da addu’ar kada ruwan sama ya sake sauka,” in ji Abbas.