Wata amarya da aka yi garkuwa da ita ana tsaka da shagulgulan bikin daurin aurenta, Farmat Paul, ta kubuta.
Da misalin karfe 10:45 na daren ranar Lahadi ne aka yi awon gaba da Farmat a gidan wani Fasto, a yayin da ake shirye-shiryen yin bikinta a yankin Ngyong na Karamar Yaying Bokkos ta Jihar Filato.
- Tsantsar jahilci ne zai sa uwa kawalcin ’ya’yanta ga ’yan bindiga
- Kotun Musulunci ta daure barawon talo-talo wata 2 a Kano
Aminiya ta rawaito cewa daga bisani an sako ta a ranar Litinin da dare, kuma nan take aka ci gaba da shagulgulan bikin nata.
Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel Ogiba, ya tabbatar da kubutar amaryar, amma bai yi karin haske kan yadda ta kubuta ba.
Idan ba a manta ba, da farko a ranar Litinin din kakakin ya bayyana cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta samu labarin sace amaryar amma ba a shigar musu da karar faruwar lamarin ba a hukumance.
Ya ce, “Ba lallai ne garkuwa da ita aka yi ba. Tun lokacin da abun ya faru babu wanda ya shigar da rahoto a wurin ’yan sanda. Mun samu labarin bacewarta kuma muna bincike a kai, amma kar a yi saurin yanke hukuncin cewa garkuwa da ita aka yi.”
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa sai da aka biya wasu kudade kafin wadanda suka yi garkuwa da Farmat su sako ta.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana can ana ci gaba da gudanar da shagulgulan bikin daurin aurenta kamar yadda aka tsara tun farko.