✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amarya ta kona kishiya da ’yarta a Kano

Matar ta ce ba ta yi nadamar sakin da mijinta ya yi mata bayan ta yi danyen aikin ba

’Yan sanda a Jihar Kano sun cafke wata amarya da ta kona uwargidanta mai suna Sha’awa Muhammad da ’yarta, ta hanyar kwara musu tafasasshen ruwa.

Amaryar wadda ta ce sakin da mijinta ya yi mata saboda abin da ya faru bai dame ta ba, ta antaya wa kishiyar da goyonta tafasasshen ruwan ne bayan ta yi zargin ’yar uwar gidan ta shiga bandaki ta zuba mata omo a ruwan da za ta yi wanka da shi.

Wacce ake zargin, mai dauke da tsohon ciki, ta bayyana cewa duk da cewar ba ta ga yarinyar ta zuba mata omo a ruwan wankan nata ba, amma ta gaskata hakan ne saboda yaran sun saba yi mata hakan.

Matar ta kara da cewa, “hakan ya sa na je wurin maigida na gaya masa, inda ya tashi ya je ya gane wa idanunsa.

“Mun koma muna magana da shi sai ga ita mahaifiyar [yarinyar] ta shigo sai ta fara magana cewa ina yawan yin korafi a kan yara.

“Ni kuma na ce mata ta yi min shiru ba da ita nake magana ba amma maimakon ta yi shiru sai ta ci gaba har tana daga murya sama.

“Hakan ya sa ni kuma na kwara mata ruwan zafi da ke cikin wani karamin bokiti da ke hannuna,” inji matar.

Mutuwar aurena shi ya fi

A cewarta, ta yi nadamar abin da ya faru, amma kuma sakin da mijin nasu ya yi mata shi ya fiye mata sauki kasancewar ba dadin auren take ji ba.

“A take da abin ya faru maigidan ya ce ya sake ni saki uku wanda kuma ni hakan ma ya yi min domin tun da na yi auren ba dadinsa nake ji ba.

“Abin da ya fi damu na shi ne halin da ita abokiyar zamana tare da ’yarta ke ciki. Wallahi na yi nadama sosai. Da na san hakan ce za ta faru da ba zan yi ma magana a kai ba.”

Sai dai uwargidan wacce ke kwance a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed ta bayyana cewa “ina yin kokarin yi mata bayani cewa ba A’isha ba ce ta yi mata laifin sai kawai ta fara min tsawa tana cewa wai kada in shiga abin da ba hurumina ba.

“Muna cikin magana sai ta fita waje, ban yi aune ba sai na ji kawai an kwara min ruwan zafi ni da yarinyar da ke kusa da ni.

“Bayan nan kuma sai ta cakumo ni tana fadin wai sai ta ga bayana; Daga nan maigidan ya kore ta waje sannan ya kwashe mu zuwa asibiti.”

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wacce ake a zargi gaban kuliya.

Ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Sheka Sabuwar Abuja da ke Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar a ranar Juma’ar da ta gabata.