✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aman wuta daga Dutse ya ci mutum 14 da kauyuka 11 a Indonesiya

Jami’an lafiya sun ce mutum akalla 56 ne suka jikkata kuma yawancinsu sun samu mummunar kuna

Yawan mutanen da suka rasu ya karu zuwa 14, wasu da dama kuma sun jikkata bayan wani dutse ya yi aman wuta a kasar Indonesiya.

Ma’aikatan lafiya a kasar sun ce mutum akalla 56, ciki har da wasu mata biyu masu ciki ne suka jikkata, kuma yawancinsu sun samu mummunar kuna.

“Kawo yanzu mutum 14 ne suka rasu,” kuma daga cikinsu an gane mutum biyu, kamar yadda kakakin Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasar Indonesiya, Abdul Muhari, ya shaida wa taron manema labarai a ranar Lahadi.

Zubar burbushin tokar dutsen da hayaki mai zafi daga aman wutar ya kawo tsaiko na wani lokaci a ranar Lahadi ga masu aikin ceto.

Ibtila’in ya faru ne bayan Tsaunin Mount Semeru da ke yakin Tsibirin Java ya yi aman wuta, inda zubar toka da dagwalon wutar suka tilasta wa dubban mazauna kauyuka 11 da ke yankin yin kaura daga muhallansu.

Bayan aman wutar a ranar Asabar, tokar ta rufe gidaje da motoci da dabbobi, lamarin da ya sa mutane da dama samun mafaka a makantu da masallatai da wuraren taruka.

A cewar Banid, wani mazaunin yankin Kampung Renteng mai mazauna kimanin 3,000, “Ba mu san cewa tabo mai zafi ba ne, kwatsam sai muka ga sama ta yi duhu, daga nan kuma sai hayaki mai zafi da ruwa suka biyo baya.”

Shugaban Kasar Indonesiya, Joko Widodo ya bayyana damuwa tare da bayar da umarnin a gaggauta ceto mutane da suka makale ko sauran abin ya ritsa da su.

Kawo yanzu dai an masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da akalla mutum 10 da suka makale a sakamakon lamarin a yankin Lumajang.