Ministan Sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya nemi afuwar ’yan kasar dangane da lalacewar da taragon da ke jigiliar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a tsakanin ranar 18 zuwa 20 ga watan Nuwamba.
Ministan ya nemi afuwar ne ranar Litinin a tashar jirgin kasa ta Moniya yayin duba aikin jirgin kasan da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.
- Titin jirgin kasa daga Kano-Nijar zai ci Dala biliyan biyu
- Za mu daure masu kasuwanci a titin jirgin kasa —Amaechi
Ministan ya umarci Kamfanin kere-kere na China Civil and Construction Company wato CCECC da suka da suka yi aikin da su sauya jiragen da wasu sabbi.
Amaechi ya ce, “Ina neman afuwar ’yan Najeriya game da abin da ya faru da jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.
“Muna da damar mayar da jiragen don haka muka kira masu kamfanin a kan su sauya mana saboda sun lalace har wajen sau uku kenan.
“Mun kuma sa an karo jiragen ne saboda daukar fasinja da yawa, amma idan haka na faruwa zai iya kawo mana tsaiko,” inji Amechi.
Bayan kusan watanni biyar da karin sabbin jirage amma sai dai sun sha lalacewa a tsakiyar daji, lamarin da ya ke barin mutane cikin zulumi da jimami.
Sai dai Ministan Sufurin ya ba wa ‘yan Najeriya tabbacin ma’aikatarsa za ta ci gaba da ingata harkar sufurin jiragen kasa a fadin Najeriya.