✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta kashe mutum 4 ta rusa gidaje 5,200 a Kano

Ambaliyar ruwan sama ta yi ajalin mutum hudu tare da rusa gidajen 5,200 a Kananan Hukumomin Rogo da Dambatta a Jihar Kano. Hukumar Agaji ta…

Ambaliyar ruwan sama ta yi ajalin mutum hudu tare da rusa gidajen 5,200 a Kananan Hukumomin Rogo da Dambatta a Jihar Kano.

Hukumar Agaji ta Jihar Kano ta ce iftila’in ya yi ajalin mutu biyu tare da rusa gidaje 5,000 a Karamar Hukumar Dambatta, da wasu biyu da suka mutu a Rogo inda gidaje 200 suka rushe.

Babban Daraktan Hukumar, Saleh Jilli ya asarar ta auku ne bayan ruwa da aka tafka tare da ambaliya a Kananan Hukumomi 20 a Jihar Kano.

“Mun tura tawagarmu domin tantance abin da ya faru muka kuma ziyarci Rogo da Dambatta domin jajantawa game da iftila’in”, inji shi.

Saleh Jilli ya ce mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu na tsugune a wurin dangoginsu a yankunan da abin ya shafa.

Ya ce hukumar ta raba kayan tallafi na Naira miliyan 3.5 ga mutanen da ambaliyar ta shafa domin saukaka musu halin da suka shiga.