✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’umuran Ruhu

Mutumin da ba ya da Ruhu yakan ki yin na’am da al’amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu…

Mutumin da ba ya da Ruhu yakan ki yin na’am da al’amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su. Mutumin da yake na ruhu kuwa yakan rarrabe da komai, shi kansa kuma ba mai jarraba shi – 1 Korantiyawa 2:14-15.

Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa zuwa gare mu. 

Barkanmu kuma da sake haduwa domin mu yi nazari daga cikin Littafi Mai tsarki a kan al’umuran Ruhu.

Littafi Mai tsarki kalmar Ubangiji ne, yana cike kuma da ikon Ubangiji kamar yadda muka gani cikin makonnin da suka gabata. Wannan kalmar Ubangiji kuma rayayyiya ce, kamar yadda muka gani cikin Littafin Ibraniyawa 4:12, “Domin maganar Allah rayayyiya ce, mai karfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu da kuma gabobi, har ya zuwa cikin bargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta.” Takan wartsaka ruhun mutum da haskenta, ta kuma bayyana haske da gaskiyar Ubangiji Allah da kan watsar da kowace irin duhun da Iblis ya sanya cikin zuciyar mutum kamar yadda Manzo Bulus ya rubuta cikin Littafin Romawa 1:6: “…domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto.” Wato idan muka ba da gaskiya ga maganar Ubangiji, za mu samu ceto. 

Al’umuran Ruhu: Akwai abubuwa biyu da nake so mu yi lura a nan, na ddya; Maganar Allah (Littafi Mai tsarki), na biyu, sani ko mu ce fahimtar maganar Allah. 

Ga marasa ganewa ga al’umuran Ubangiji, maganar Allah wauta ce domin ba su fahimce ikon da ke cikinta ba, don halin mutuntaka/zunubi da ke cike cikin rayuwarsu. Sha’awace-sha’awacen jiki/kayan duniya sun rufe wa dan Adam idanun da zai ga hasken da ke cikinta.

Sanin al’umuran Ruhu kuwa na bayyane ga wanda ya nema ya san ikon da ke cikin manganar Ubangiji cikin LittafinSa Mai tsarki. “Kowane nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa da tsawatarwa da gyaran hali da kuma tarbiyyar aikin adalci, domin bawan Allah ya zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.” 1 Timoti 3:16-17. Ganewarsa (al’umuran Ubangiji) kuma na bayyanuwa ga duk wanda ya bukaci Ruhu mai tsarki ya mallaki rayuwarsa.

Muna cikin wani zamani ne mai yayi, zamani da ke cike da harkoki iri-iri na rayuwa wadanda idan ba ka yin irin wannan harkoki, wadansu mutane na iya ce maka ba ka waye ba, ko su ce ba za ka more wa rayuwar nan ba har ka mutu. Musamman matasa, ana cikin wani irin yayi ne na bin al’umuran jiki da ake koya ta wurin hulda da abokai da talabijin da intanet da makamantansu. Mutane da dama sun bar al’umuran Ubangiji an koma ga jiki, ga wadansu al’umuran Ubangiji wauta ne a gare su. Bari mu ga bambanci tsakanin al’umuran jiki da na ruhu.  

Galatiywa 6:16-25, maganata ita ce: “Ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba. Don halin mutuntaka gaba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da halin mutuntaka. Wadannan biyu gaba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so. In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, shari’a ba ta da iko da ku, ke nan. Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci da aikin lalata da fajirci da bautar gumaka da sihiri da gaba da jayayya da kishi da fushi da son kai da tsaguwa da hamayya da hassada da buguwa da shashanci da kuma sauran irinsu. Ina fadakar da ku kamar yadda na fadakar da ku a da, cewa masu yin irin wadannan abubuwa, ba za su samu gado a Mulkin Allah ba.

Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamun kai. Masu yin irin wadannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su. Wadanda kuwa suke na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha’awace-sha’awace iri iri. In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al’amuranmu ta wurin ikon Ruhu.”

Wajibi ne a zamanka na mai bin Yesu Almasihu ka nemi sanin al’umuran Ruhu mai tsarki, ka kuma nuna wa dukan duniya cewa akwai nasara da iko da kuma rai madauwami cikin rayuwa cikin sanin al’umuran Ubangiji. Dogararka kuma ga Ubangiji ta zama a bayyayne ga dukan duniya. Ubangiji kuma zai cika ka da RuhunSa mai tsarki don al’umma ta ga haskenSa zai kuma ba ka nasara cikin rayuwarka. Kamar yadda Littafi Mai tsarki ke fadi: “Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah Ya yi mana baiwa hannu sake. Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar dan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al’amura masu ruhu ga wadanda suke na ruhu.” 1 Korintiyawa 2:12-13.

Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ikon ganewa cikin al’umuranSa, amin.