Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kasar nan za ta iya fitar da mutuum miliyan 100 daga talauci idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata.
Buhari ya ce “Akwai alaka tsakanin talauci da koma bayan tattalin arziki da cin hanci da kuma rashin zaman lafiya,” Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a ranar bikin cika shekara 20 da kawo karshen mulkin soji a Najeriya.
Shugaba Buhari, wanda ya fara wa’adi na biyu a karshen watan Mayu ya ce tun da kasashen China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya ci gaba.
Ya kara da cewa “Kasashen China da Indonesia sun ci gaba karkashin tsarin mulkin mulukiya yayin da India ta kai gaci a karkashin tsarin demokuradiyya, a don haka muma babu abin da zai hana mu mu kai ga gacci”.
Sai dai bai yi wani cikakken bayani kan yadda gwamnati za ta yi hakan ba, abin da ya sa wasu ke ganin kalamai ne kawai irin na ‘yan siyasa da sukan yi domin birge jama’a ko jan hankalin masu sauraransu.
Wannan ne karon farko da ake yin bikin Ranar Demokuradiyyar a ranar 12 ga watan Yuni.
An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma “rage radadin” alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993.
Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojan na wajan lokacin ta soke.
Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la’akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan.