✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar garin Abbare na neman dauki

A farkon wannan makon ne al’ummar garin Abbare da ke Karamar Hukumar Lau a Jihar Taraba suka rubuta takardar koke zuwa ga hedikwatar tsaro ta…

A farkon wannan makon ne al’ummar garin Abbare da ke Karamar Hukumar Lau a Jihar Taraba suka rubuta takardar koke zuwa ga hedikwatar tsaro ta kasa da suka hada da ofishin shugaban soja da shugaban ‘yan sanda na kasa dangane da yadda wasu masu sanye da kayan sojoji suka harbe masu shanu sama da 100.

Mai magana da yawun al’ummar garin Abbare, Alhaji Muhammed Sale wanda daya ne daga cikin wadanda suka sanya hannu a takardar koken, ya shaidawa wakilinmu cewa masu saye da kayan sojojin sun shiga yankin Abbare ne a cikin motoci soja wasu kuma akan Babura, inda suka kashe masu shanu.

Ya ce isar masu sanye da kayan sojojin yankin ke da wuya, sai suka  bude wa shanun da suke kiwo a wani daji da ke Arewa da garin Abbare wuta, inda suka kashe shanu sama da 100, sannan kuma wasu guda 500 suka watsu cikin daji, kuma har yanzu ba a same su ba.

Alhaji Muhammed Sale ya bayyana cewa abin da ya daurewa al’ummar garin na Abbare kai dangane da wannan ta’asa shine kasancewar ba wata rigima tsakaninsu da  wata kabila a yankin, kuma dabbobinsu ba su shiga gonar kowa sun yi barna ba, amma ssai ga shi da rana tsaka wasu sanye da kayan sojoji sun shiga yankinsu sun kashe masu dabbobi haka siddan.

Ya kara da cewa lokacin da mutanan ke harbin shanunsu, matasa sun yi yunkurin fito na fito da su, amma sai su dattijan garin suka hana. “Ga dukkan alamu manufar maharan ita ce su halaka al’ummar garin na Abbare amma sai Allah ya kare su,” inji shi.

Ya bayyana cewa tun lokacin da aka fara fada tsakanin fulani makiyaya da ‘yan kabilar Bachama wadanda ke Jihar Adamawa a bara wanda daga bisani fadan ya shiga yankinsu, inda aka halaka mutanen su sama da 70 tare da kone gidajensu fiye da 200.

Ya ce sojojin sa kai na kabilan Nyandan da Baali da Bachama sun sace masu shanu sama da dubu daya amma har suna cigaba da halaka Hausa/Fulani akan hanyoyin mota da na zuwa wurin kiwo da gona a yankin, kuma ba a kama kowa ba ko hukunta wani ba.

Alhaji Muhammed Sale ya ce abin takaicin shi ne a maimakon hukuma ta kama masu kashe mutane, sai kuma aka juya ana kama al’ummar Hausa/Fulani wadanda sune ake zalunta.

“Bukatar masu kai masu harin wadanda ke da goyon bayan wasu ‘yan siyasan yankin shi ne a kori al’ummar Hausa/Fulani a yankin. Don haka fatanmu shi ne hukuma ta gano gaskiyar ko su wanene suka kawo mana hari don a hukuntasu. Domin daukacin jama’ar garin Abbare suna zaune a cikin fargaba, kasancewar ba wanda ya san manufar maharan da wanda ya tura su,” inji shi.