✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Almakashin tiyata ya shekara 23 a cikin wata mata

Wata mata mai suna Ezeta Gobeeba mai kimanin shekara 62 daga yankin Arewacin Ossetia a kasar Rasha ta shafe shekara 23 tana fama da ciwon…

Wata mata mai suna Ezeta Gobeeba mai kimanin shekara 62 daga yankin Arewacin Ossetia a kasar Rasha ta shafe shekara 23 tana fama da ciwon cikin sakamakon almakashin tiyata da likitoci suka manta a cikinta bayan yi mata tiyata.

Ezeta Gobeeba, wadda a yanzu take karbar kudin fansho bayan yin ritaya daga aikinta, ta jima tana fama da ciwon ciki, bayan tiyatar da aka yi mata a 1996, inda da zarar ta ziyarci asibiti sai likitocin su ce, mata ciwon hanta ne ke damunta, babu abin da za su yi, sai da su yi ta ba ta magungunan da za su kashe radadin ciwon.

Sai a kwanakin baya ne a asibiti aka bayar da umarnin a yi wa Ezeta, hoton sassan jiki D-Ray don gano ciwon da ke damunta a ciki, bayan ta ci gaba da bayyana irin ciwon cikin da ke damunta, inda ta ce ko ta sha magani sai dai kawai ya rage zafin ciwo, amma ciwon cikin na nan.

Bayan daukar hoton likitocin sun gano akwai tarin karafunan tiyata da suka hada da alkamashi, wanda ya yi sanadiyyar ciwon cikin. Ezeta, ta ce tun lokacin da aka yi mata tiyata shekara 23 da suka wuce take fama da ciwon ciki.

Ezeta Gobeeba, ta bayyana wa jaridar kasar Rasha mai suna Komsomolskaya Prabda cewa, a lokacin da mai amfani da na’urar daukar hoton D-Ray, ya yi tunani Ezeta, ta shiga dakin hoton da wadannan karafunan tiyatar ce.

Likitar ta ce, “Hoton cikin Ezeta, na nuna akwai alkamashi, sai Ezeta ta ce, mene ne alkamashi? Sai likitar ta nuna min hoton cikin da ke nuna alamar alkamashi a cikinta, sai na firgita hakan ya sa na fara kuka, abin da ke damuna ke nan a ciki na wadannan shekaru,” inji Ezeta.

Wadannan karfuna da suke cikin Ezeta, likitoci suna amfani da su wajen cire wasu abubuwan jikin mutum lokacin yin tiyata, amma daga bisani an sanya wa Ezeta ranar da za ta je asibiti don cire abin da ke damunta. Ezeta ta kara komawa asibitin an yi mata tiyata an cire dukan karafunan da suke cikinta. Kalubalen da ake samu wajen likitoci lokacin yi wa marasa lafiya tiyata, yana daya daga cikin abin da yake ci wa kasar Rasha tuwo a kwarya, musamman Arewacin Ossetia, don haka Ma’aikatar Lafiya ta kaddamar da bincike na musamman kan lamarin.

Kakakin Ma’aikatar Lafiya, ta tabbatar wa jama’a cewa Ministan Lafiya na kasar da kansa yana lura da binciken da ake gudanarwa game da wannan matsala. Kuma ta ce hukumomi ne za su biya kudin tiyatar da aka yi wa Ezeta, sannan a biya ta kudin jinyar da ta yi na wannan shekarun da ta yi tana fama da ciwon.