✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mallam Sama’ila Isa Funtua ya rasu

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na hannun daman Shugaba Buhari, Mallam Sama'ila Isa Funtua ya rasu.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, daya daga cikin mukarraban Shugaba Buhari, Mallam Sama’ila Isa Funtua ya rasu.

Sama’ila Isa Futua ya rasu ne a Abuja sakamakon ciwon zuciya a daren Litinin 20 ga watan Yuli 2020, kamar yadda wani dan uwansa ya tabbatar.

“Ya gaya wa iyalansa cewa zai je ganin likita amma ya biya ta wurin mai aski. Shi ya rika kansa zuwa asibiti”, dan uwan nasa ya shaida wa wakilinmu.

Ana sa ran a safiyar Talata za a sallaci gawarsa, wadda wata majiya ta ce an kai ta masallacin Area 1 a’a Abujar.

Marigayin tsohon minista ne a Najeriya kuma tsohon shugaban kungiyar masu gidajen jaridu na Najeriya (NPAN).

Mallam Sama’ila kuma dan jarida, ɗan kasuwa ne sannan kwararre a fannin gudanarwa.

Allah Ya gafarta Ya ku rahamshe shi, amin.

%d bloggers like this: