Allah Ya yi wa Alhaji Amadu Kurfi, tsohon Sakataren tsohuwar hukumar zaɓe (FEDECO) rasuwa.
Alhaji Amadu Kurfi ya rasu ne yana da shakara 90, a daren ranar Laraba bayan ya yi fama da jinya.
A lokacin rayuwarsa, marigayin shi ne Maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi na farko.
Shi ne kuma ne wanda ya fi kowa yawan shekaru daga cikin hakiman Masarautar Katsina.
Za a yi jana’izarsa ranar Alhamis ɗin nan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.