✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya ba Yusuf Buhari lafiya- Gudloock Jonathan

Tsohon Shugaban Kasa Gudloock Jonathan ya jajintawa iyalan Shugaba Buhari da ‘yan Najeriya bisa hadarin da Yusuf Buhari ya samu na babur, inda ya samu…

Tsohon Shugaban Kasa Gudloock Jonathan ya jajintawa iyalan Shugaba Buhari da ‘yan Najeriya bisa hadarin da Yusuf Buhari ya samu na babur, inda ya samu rauni.

A cewar tsohon shugaban, “Ina Kasar Laberiya inda nake ci gaba da aikin sa ido a kan zabe sai kwatsam na samu wannan mummunan labarin.

“Da ni da iyalina muna yi wa Yusuf addu’ar samun sauki. Sannan kuma ina kira ga sauran ‘yan Najeriya da su ajiye duk wani bambanci domin mu hadu mu nuna wa iyalan shugaban kauna,” in ji Gudloock Jonathan.