Idan kome ya tafi kamar yadda aka tsara bisa ga jigilar dawo da alhazan kasar nan na bara, su kimanin 76,000, (66,000, na Hukumomin Alhazai na jihohi 10,000, na `yan jirgin yawo), ina fata zuwa wannan lokaci da mai karatu ya ke karanta wannan makala, an kammala jigilar alhazan gaba daya, idan ma ba a kammala ba, to dan burbushen da ka rage ka iya kasancewa jami’an hukumomin jin dadin alhazai na kasa da na jihohi ne da suka kula da aikin hajjin.
Aikin Hajjin bara, aiki ne da a cikin shekaru 25, da suka gabata, ya kasance mafi muni na farko da aka taba samu akan annobar rasa rayuka da jikkatar daruruwan maniyata a kasar ta Saudiyya. A Hajjin shekarar 1990, a ranar 2 ga watan Yulin wannan shekarar, an samu mutuwar maniyata 1426, bayan turmutsitsin hanyar kasa da aka samu, a sanadiyar daukewar wutar lantarki. A aikin Hajjin bara sau biyu cikin kwanaki 13, aka samu munanan hadurra. Hadarin farko da aka samu shi ne,na ranar 11 ga watan Satumbar da ya gabata, wanda kugiyar gini a cikin Haramin Makka ta fado wa maniyata masu dawafi, al`amarin da ya haddasa mutuwar maniyata 111, wasu kuma suka jikkata. Sai kuma na ranar babbar Sallah, wato 24 ga dai watan na Satumba, wanda a lokacin jifar Jamrah, a wani turmutsitsin maniyata, wanda aka kiyasta zuwa yanzu mutane sama da dubu biyu da121, ake zargin sun mutu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya kalato a baya-bayannan, baya ga daruruwan da suka jikkata, yayin da wasu daruruwan suka bace, ana ta fafutikar nemansu.
Idan aka hada jimlar wadanda suka mutu daga hadarin fadowar kugiyar gini 111, da 2,121,, na turmutsitsin jifar Jamrah, za a ga cewa Maniyata, 2,232, ke nan suka mutu a bana, baya ga wadanda suka jikkata, da wadanda ake nema. Zuwa yanzu Hukumar Jin Dadin Alhazai ta kasa, wato NAHCON, ta bakin Kwamishinanta mai kula da shirye-shirye da yada labarai, Dokta Saleh Okenwa, ya shaida wa manema labarai a Makkah ranar Litinin din nan cewa, Maniyatan kasar nan 199, suka mutu, wasu 121, suka bace, biyar kuma suna kwance a asibitoci daban-daban. Kodayake akwai zargin wadanda suka bacen sun mutu, duk kuwa da ba iya ganin gawarwakinsu ba a cikin wadanda suka mutun, amma dai Hukumar ta NAHCON ta dage akan ba za ta sa su cikin jerin wadanda su ka mutum ba, har sai mahukuntar kasar ta Saudiyya sun kammala binciken kimiyya na hoton yatsunsu ko kuma gwajin kwayoyin halittarsu.
A rahoton AP, Maniyata 2,121, da suka mutu a turmutsitsin Jamrah sun fito ne daga kasashe 30, daga cikin 180, na duniya da suka yi aikin Hajjin barar. kasar Iran ita tafi rashi, inda ta rasa maniyata 465, sai kasar nan mai Maniyata 199, ya yin da ta Mali ta ke da 198. Mu a nan cikin gida jihar Sakkwato ake kyautata zaton ta fi yawan Maniyatan da suka mutu, su kimanin 79, kodayake Muhukuntar jihar sun ce Maniyatansu da suka mutu sun kai 100. Jihar Kano na da Maniyata 20. Daga cikin kuma manyan mutanen da suka mutu a turmutsitsin daga nan kasar akwai Mai martaba Sarkin Zing kuma shugaban ayarin maniyatan jihar Taraba Alhaji Abbas Sambo da matansa biyu da wasu iyalensa biyar, akwai masu shari`ar Kotun daukaka kara, Mai shari`a Abdulkadir Jega da Mai shari`a Musa Hassan Alkali da Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar koli ta harkokin addini Islama na kasa baki daya, kuma Malami a Jami`ar Maiduguri Farfesa Tijjani Abubakar El-Miskin da shahararriyar `yar jaridar nan Hajiya Bilkisu.
Afkuwar turmutsitsin ke da wuya sai kasar Saudiyya ta zargi Maniyatan kasashen bakaken fata na nahiyar Afirka da cewar su suka haddasa turmutsitsin, bisa ga kasa bin ka`idar lokacin da aka tsara su zo wajen jifar. Ko mahukuntan sun manta, ko kuma suna sane da cewa a ranar farko ta jifar Jamrah, wadda ta ke ranar Babbar Sallah ce, maniyata kwararowa suke da fatan a wannan safiyar sun gama aikin Hajjin da aniyar su yi jifa, su wuce Harami su yi dawafi da aski, su kwance Harami, ga masu azama, har sallar Idin ranar suke samu.
Wannan zargi ya harzuka shugabannin kasar nan da dama cikinsu kuwa har da Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II, wanda kuma shi ke jagoran maniyatan kasar nan a bana, wanda tunda tirmitsitsin ya faru da rana daya Sarkin Kanon bai taba rufe bakinsa ba wajen kiran mahukuntar kasar ta Saudiyya da lallai su tsaya, su ga sun gyara irin tsarin da ake raba Hema a zaman Mina, inda Maniyatan kasashen bakaken fata suke can ihunka banza, ta yadda sai sun shafe awa daya zuwa biyu, kafin su zo wajen jifa, alhali sauran maniyatan kasashen fararen fata (Larabawa), bayan dukkansu sun kasance kusa da Jamrar, wasu ma Tantunansu a jikin Jamrah suke. Har sai da ta kai fagen da Maimartaba Sarkin na Kano tun yana kasar ta Saudiyya da bayan ya dawo nan gida ya tara Maluma, inda ya nemi su kawo fatawar akan zaman maniyata a Mina, ya kuma sha alwashin kiran taron Maluman na kasa baki daya akan yadda za a warware wannan maslahar ibada.
Sarkin na Kano kuma jagoran maniyatan banan ya sha nanata cewa muddin kasar ta Saudiyya ba za ta iya ba maniyatan kasar nan wurare kusa da Harami a yayin zaman Mina ba, to kuwa a aikin Hajji na gaba, to, su bar maniyatan kasar nan su zauna Makkah, su rika tafiya jifar Jamrah daga Makkan. Haka ma a masaukan da akan kama wa maniyatan kasar nan a Makkah, su ma San Kanon ya koka akan irin yadda suke nesa da Harami, ta yadda akasarin maniyata, musammaan masu rauni, ba sa jurewa tafiyar su je su dawo, ta yadda wasu in sun fita zuwa Harami da safe, sai bayan sallar Isha`i su ke komawa masaukansu, wannan ma batu ne da Sarkin y ace lalle a duba a kuma gyara.
A lokacin da ake zaman jiran abinda taron Maluman zai fito fa shi akan zama Makkah maimakon na Mina ga maniyatan kasar nan da kuma irin yadda mahukunta za su bullowa kama masaukai kusa da Harami a birnin na Makkah, da kuma jiran cikakken rahoton abin da ya haddasa wancan turmutsitsi da yawan mutanen da suka mutu, ko suka jikkata da yadda kasar ta Saudiyya za ta biya diyya. Wasu batutuwa biyu da za su saukaka wannan dambarwar zaman Mina kusa da Jamrah da samun masaukai kusa da Harami a Makkah ga maniyatan wannan kasa, a tawa fahimtar bai wuce fara shirye-shiryen aikin Hajji da wuri, da kuma maniyata su kwan da shirin za su samu karin biyan kudaden kujera fiye da yadda suke biya yanzu. Tarihi ya tabbatar da cewa sama da shekara 30, kowa ya san unguwanni da jihohin kasar nan suke ajiye maniyatansu irin su Shara Mansur da Shara Sittin da Kudai da sauransu, su dai ne duk shekara ba canji. Haka kuwa yana faruwa ne akan rashin fara aikin Hajjin kowace shekara da wuri da Hukumar NAHCON ba ta yi, wanda a lokacin da mu za mu fara za ka tarar Mahukuntan kasashe irinsu Indunisiya da Iran da Pakistan, tuni sun kame, sun kuma biya masaukan da ke kusa da Harami. A lokacin da ni ke addu`ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu, Ya kuma tashi kafadun wadanda suka jikkata, tare da bayyana wadanda suka bace.
Ina kuma rokon Allah da kar Ya sake maimaita mana annobar da ta faru a aikin Hajjin shekarar 1436BH wato 2015, amin summa amnin.