✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkawuran NLC ba za su cika a lokaci guda ba — Gwamnatin Tarayya

NLC ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin mako biyu don daidaita farashin kayan masarufi.

Gwamnatin Tarayya ta ce ba abu ne mai sauki ba wajen zartar da wasu daga cikin bukatun Kungiyar Kwadago ta NLC da aka suka cimma a watan Oktoban 2023 a lokaci guda ba.

Karamar Ministar Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce, ta bayyana haka a ranar Juma’a.

Ta kara da cewa daya daga cikin yarjejeniyar da aka kulla da ke neman a samar da cibiyoyin sauya motoci zuwa masu amfani da iskar gas zai dauki lokaci kafin cibiyoyin su wadata ko ina.

Kazalika ta ce kwamitin da ke kula da samar da cibiyoyin yana aiki tukuru, don ganin an cika wannan alkawari da aka daukar wa NLC a shekarar da ta gabata.

A watan Oktoban bara ne dai, Gwamnatin Tarayya da NLC suka cimma jerin yarjejeniyoyi da suka kunshi rage wa ‘yan Najeriya radadin talauci da fatara biyo bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi.

Sauran bukatun sun hada da ɗaga darajar Naira da tashin farashi da kuma matsalar tsaro da dai sauransu.

Kungiyar kwadago dai ta bai wa gwamnati wa’adin mako biyu da ta cika alkawuran da ta daukar mata ko ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Hakan dai ya biyo bayan koke-koke da zanga-zanga da wasu ‘yan Najeriya suka gudanar a makon nan kan tashin gwauron zabi da kayan masarufi ke yi.