✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkalin Alkalan Najeriya ne yake jagorantar karar zaben Buhari da Atiku

Babban Akalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Mohammed ne yake jagorantar sauraron daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar…

Babban Akalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Mohammed ne yake jagorantar sauraron daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar suka shigar a gaban Kotun Kolin Najeriya domin kalubalantar nasarar shugaba Buhari a zaben ranar 23 Fabrairu 2019.

Kotun kolin Najeriyar ta gabatar da mambobin mutum bakwai wanda Babban Alkalin Alkalan Najeriya Ibrahim, yake jagoranta sauran Alkalan sun hada da: Bode Rhodes-Vivour, Amiru Sanusi, Uwani Abaji, Ejembi Eko, John Inyang Okoro da Olukayode Ariwoola.

Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP suna kalubalantar shari’ar da kotun sauraron kararrakin zaben tayi wanda Mai Shari’a Mohammed Garba, ya jagoranta ranar 11 ga Satumba 2019.  Wanda hakan yasa aka bai wa Shugaba Buhari nasarar zaben da aka yi.