✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkalan wasa suna samun kulawar da ta dace a Jihar Nasarawa – Shugaban kungiyar

Shugaban kungiyar Alkalan wasan kwallon kafa a Jihar Nasarawa Alhaji Adamu danjuma da aka fi sani da Amore ya ce kungiyar tana inganta kwazon alkalan…

Shugaban kungiyar Alkalan wasan kwallon kafa a Jihar Nasarawa Alhaji Adamu danjuma da aka fi sani da Amore ya ce kungiyar tana inganta kwazon alkalan kwallon kafa a jihar ne ta hanyar shirya wasanni a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa daban daban dake jihar.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Lafiya game da harkokin kungiyar a jihar. Ya ce kodayake akwai abubuwa da dama da kungiyar take yi don inganta kwazon alkalan wasan kwallon kafa a jihar a kodayaushe. Ya ce sau da yawa kungiyar ta fi bada fifiko ne wajen hada kai da kungiyar kwallon kafa a jihar karkashin shugabancin Alhaji Mohammed Alkali inda suke shirya wasanni a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a jihar kuma suke amfani da alkalan wajen hura wasanni don inganta kwazonsu.
Ya ce a yanzu haka ma akwai wasan kwallo da suka shirya tare da hadin gwiwar kungiyar kwallon kafa a jihar inda wadannan alkalai za su yi alkalanci&nbsp don inganta kwazonsu.
Ya ce a halin yanzu kimanin alkalan wasan kwallon kafa 16 ne suka samu karin girma inda a yanzu suke da dama su yi alkalanci a ciki da kuma a wajen jihar.
Ya ce ayyukan kungiyar sun hada da kawar da cin hanci da rashawa a tsakanin alkalan da kai karar duk wani alkalin wasa da aka same shi da laifin nuna son kai a lokacin hura wasa ga kungiyar ta kasa don hukunta shi da dai sauransu.
Daga nan sai ya yi amfani da damar inda ya jinjina wa shugaban kungiyar kwallon kafa ta Jihar Alhaji Mohammed Alkali dangane da cikakken goyon bayan da yake ba kungiyar alkalan wasan don ganin an samu biyan bukata.