Alkalai sun titsiye Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino kan zargin almundahana, wata biyu kafin a zabe shi ya jagoranci hukumar a karo na uku a jere.
Sabuwar dambarwar ta taso ne a yayin da shugaban na FIFA ke fuskantar zargin kawo cikas ga shari’ar manyan laifuka da kuma tunzuri da nufin keta haddin hukuma.
Daya daga ciki alkalai biyu da suka yi wa Mista Infantino tambayoyi, Hans Maurer, ya ce, “Gaskiya ne, ni da (Ulrich) Weder mun yi wa Mista Infantino tambayoyi.
“Sai dai ba zan bayyana dalilin tambayoyin da kuma lokacin da zaman ya gudana ba,” in ji sakon imel din da Hana Maurer ya aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Tun a tsakiyar shekar 2020 shugaban na FIFA ke fuskantar zargin “kuma kawo cikas ga shari’ar manyan laifuka, tunzuri da nufin keta haddin hukuma, da kuma rashin boye sirrin ofis.”
A ranar Laraba, kafofin yada labarai na Le Monde da kuma Sueddeutsche Zeitung sun ruwaito cewa a ranar Talata aka binciki Infantino a birnin Zurich, fadar FIFA.
Alkalan Switzerland na zargin Mista Infantino da yin ganawar sirri sau uku da tsohon Shugaban Hukumar Shari’a kuma Antoni-Janar ma kasar, Michael Lauber.
Sai dai shugaban na FIFA ya dage cewa gawarsa da Michael Lauber ta yau-da-kullum ce.
Wannan ka-ce-na-ce ne ya sa Mista Lauber ya yi murabus daga matsayinsa, a daya bangaren kuma, Hukumar FIFA ta wanke Infantino daga aikata ba daidai ba.
Tazarcen Infantino a FIFA
A watan Maris na bana ne za a zabi Infantino ba tare da hamayya ba, domin fara wa’adinsa na uku a matsayin shugaban FIFA.
Za a zabe shi ne a Babban Taron FIFA karo na 73 da zai gudana a Kigali, babban birnin kasar Rwanda ranar 16 ga watan Maris.
Da haka Infantino zai zama mutum na uku a tarihi da ya shugabanci FIFA sau uku, bayan Joao Havelange (1974-1998) da kuma Sepp Blatter (1998-2015) — wanda Infantino ya zama magajinsa.
A shekarar 2016 FIFA ta zabi Infantino inda ya yi alkawarin dawo da martabarta, bayan zargin almundahana da ya dabaibaye wa’adin karshe na Sepp Blatter.