✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ali Nuhu ya samu kyautar mai tallafa wa gwarzon jarumi

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da bikin gasar Nigeria Entertainment Award (NEA Awards) a birnin New York da ke Amurka, inda…

Ali Nuhu rike da kambinsaA ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da bikin gasar Nigeria Entertainment Award (NEA Awards) a birnin New York da ke Amurka, inda fitaccen jarumi Ali Nuhu ya samu kyautar mai tallafa wa gwarzon jarumi.
Wannan bikin shi ne karo na 8 kuma an gudanar da shi ne a dakin taro na Skirball Performing Centre da ke jami’ar New York ta Amurka.
Ali Nuhu ya fafata a gasar ne wajen neman Gwarzon Jarumi da fim din ‘Confusion Na Wa’ da kuma mai tallafa wa gwarzon jarumi da fim din ‘Blood And Henna’, a karshe jarumin ya yi nasara da fim din ‘Blood And Henna’.
Yadda aka gudaar da zaben kuwa shi ne- ‘yan kallo ne suka zabi gwanayensu ta intanet, an kuma fara zaben ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2013. ‘Yan kallo sun zabi mawaka da ‘yan fim da ‘yan kama (comedians) da sauransu a Najeriya.
Bayan an sanar da sakamakon zaben ne a wurin taron jarumin ya sanar a shafinsa na facebook da kuma twitter, inda ya bayyana farin cikinsa.
Furodusan ‘Blood And Henna’, Kenneth Gyan ma ya sanar da nasarar da jarumin ya samu, sannan ya bayyana farin cikinsa.
A yayin bikin mawaka da suka hada da Tiwa Sabage da Iyanya da Emma Nyra ne suka gudanar da wakoki.
An fara gudanar da wannan gasar ne a shekarar 2006 a New York don mawaka da ‘yan kama da masu shirya fina-finai a Afrika musamman na Najeriya.
Kafar yada labarai ta BellaNaija da kuma kamfanin jirgin sama na Arik Air ne suka dauki dauyin shirya wannan bikin.