✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alhassan Doguwa ya lashe zaben Majalisar Tarayya karo na biyar

Tun a shekarar 2007 Honarabul Doguwa ya shiga zauren majalisar.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Honarabul Alhassan Ado Doguwa, ya lashe zaben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada na Jihar Kano.

Tun a shekarar 2007 Honarabul Doguwa ya shiga zauren majalisar, inda a yanzu ya zamana cewa ya lashe zaben kujerar karo na biyar a matsayin mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada a matakin Tarayya.

Da yake sanar da sakamakon, Baturen Zaben Farfesa Sani Ibrahim ya bayyana cewa Doguwa ya samu kuri’u 41,573 don haka shi ne ya zama zakara.

Babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar NNPP, Air Commodore Salisu Yushau wanda yazo na biyu ya sam kuri’u 34,831.

Tun a ranar 25 ga watan Fabrairu ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gudanar da zaben ’yan Majalisar Tarayya, inda ta ayyana zaben mazabar Doguwa/Tudun Wada a matsayin wanda bai kammala ba.

A wancan lokaci dai INEC ta ce ta yanke wannan hukunci ne sakamakon aringizon kuri’u da kuma tashe-tashen hankula da aka samu a lokacin zaben musamman a wasu daga cikin mazabun garin Tudun Wada.

Haka kuma, a lokacin da yake sanar da sakamakon zaben na watan Fabrairu, Baturen Zaben Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya bayyana cewa ya sanar da sakamakon zaben ne bisa tursasawa.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan shi ne dalilin da a yau Asabar INEC ta sake gudanar da zaben domin tabbatar da sahihancin sakamakonsa.

A halin yanzu dai Alhassan Doguwa na daya daga cikin masu neman takarar Kakakin Majalisar Wakilai ta 10 da nan wani lokaci kadan za a gudanar da zabe.