✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alhakin kare rayuka

A yanzu hare-hare a kan farare hula sai kara kamari suke yi, idan ba za a manta ba dai an kai hari mafi muni Kwalejin…

A yanzu hare-hare a kan farare hula sai kara kamari suke yi, idan ba za a manta ba dai an kai hari mafi muni Kwalejin Koyar da Noma da ke Gujba, Jihar Yobe a ranar Lahadi 29 ga Satumba, 2013 inda dalibai suna barci aka tashe su bayan an jera a layi ne aka rika harbinsu daya baya daya, a wurin kawai an kashe fiye da 41, daga baya kuma aka rika tsintar gawarwaki a daji da ke kusa da makarantar. Bayan nan kuma maharan suka kona wadansu gine-ginen makarantar.
A wani harin makamancin irin wannan a watan Yuli cikin wannan shekarar an sake kashe wadansu daliban a wata makarantar kwana da ke Mamudo a Jihar Yobe. A watan Mayu ma an kai hare-hare wadansu makarantun sakandare biyu da makarantar firamare a Maiduguri inda aka kashe malamai 3 aka raunata dalibai masu yawa. A Mubi da ke Jihar Adamawa an kashe fiye da dalibai 30 a bara. An alakanta wadannan hare da ‘yan Boko Haram wadanda aka fara rikici da su tun shekarar 2009. ‘Yan kungiyar sun dauki alhakin kai wadansu daga cikin hare-hare inda suka bayyana hakan a shafinsu na intanet.
Kodayake ba wai makarantun ba ne kananan danga masu dadin tsallakawa a wurin maharan ba. Abin mamaki da daure kan shi ne an sanya jami’an tsaro sakamakon sanya dokar ta-baci a wannan jihohi inda jami’an tsaro suka rika farautar maharan amma kuma sai suka rika huce haushinsu a kan ‘yan kauyuka. Mako daya ko biyu kafin a kai harin Gujba maharan suka tare hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Benisheikh inda suka kashe mutane fiye da 150 ciki har mata da kananan yara.
Abin daure kan shi ne duk wadannan abubuwan sun faru ne a jihohi da Shugaba Jonathan Goodluck ya kafa dokar ta baci tun cikin wata Mayu.  Tabbas za a iya cewa jami’an tsaro sun dan ci karfin ‘yan Boko Haram inda suka farraka su sai dai wadanda suka rage har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare a kauyuka. Bugu da kari ga wadansu matasa ’yan sa kai suka sha alwashin farautar ‘yan Boko Haram da ake kira Cibilian JTF.
Wani abu da yake bukatar tambaya shi ne ta yaya duk da shingayen jami’an tsaro amma ake ci gaba da kai wa hare-hare. Ta yaya ‘yan bindiga cikin tawagar motoci su yi tafiya mai nisa su kuma kaddamar da hare-hare ba tare da jami’an tsaro sun gano ba?
Tun bara da aka fara kai hare-haren makarantun da an tsaurara matakan tsaro a makarantun, amma ba a yi hakan ba. Misali a Gujba da an tsaurara matakai da abin bai kai ga haka ba. Hana amfani da wayar sadarwa ma ta fi illa a kan amfanin hakan wurin magance matsalar tsaro. Idan an bar wayar sadarwa jama’a za su rika amfani da su wurin kira ko aika sakonni a duk lokacin da suke zargin faruwar wani mummunan abu.
Don haka ya kamata hukumomi sun janye dakatarwa hana amfani da wayar salula, ko ba za a dawo da amfani da wayar salular ba gaba daya, to a daga kafa lokaci zuwa lokaci, domin jama’a suna cikin kunci. Gwamnatin wadannan jihohi sun yi namijin kokari wurin bude makarantun duk da cewa ‘yan Boko Haram suna ci gaba da kai hare-haren bayan sun yi ikrarin duk wani abu da ya shafi karatun boko haramun ne.
Idan har da gaske abin da suke ikrarin gaskiya ne da sun daina amfani da bindigogi da wayar hannu da tuka motoci da kuma aika sakonni ta shafin intanet na You Tube, wadanda a dalilin karatun boko aka same su.
Da sun ci gaba  da mayar da hankali wurin tsayawa a kan akidarsu amma ba wai su rika kashe wadanda suke da akidar yin boko ba. Haka bai kamata su rika huce haushinsu a kan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba musamman ma mata da kananan yara. ‘Yan Boko Haram sun yi watsi da shirin tattaunawar da gwamnati ta yi yunkurin yi da su, inda suka rika kai wa hare-hare a maimakon su taimaka a samu zaman lafiya.  A yanzu dai babu tabbacin za a iya murkushe ‘yan Boko Haram cikin kankanen lokaci.
Za a kawo karshen wadannan hare-haren idan aka yi amfani da jami’an tsaro na sirri, a kuma samu hadin kan jama’a, sannan jami’an tsaro suka aiki tsakaninsu da Allah.
A tsaurara matakan tsaro a makarantun boko da ke kauyuka da gundumomi da unguwanni da garuruwa, a tabbata ba a sake kai hari makarantun ba. Yin hakan ya rataya a wuyan gwamnati. Alhakin kare rayuka ya rataya a kan gwamnati.