Wani alhajin Jihar Sakkwato da yanzu haka yake birnin Madina na kasar Saudiyya, Alhaji Arzika Bakaya, ya mayar da wasu kudi da ya tsinta kimanin Naira N400,000, mallakin wani alhajin Jihar Kaduna.
Kudin da ya tsinta su ne Dalar Amurka 700 da Naira 70,000 da kuma Riyal din Saudoyya hudu.
- Rukuni na 2 na maniyyatan Kano sun tashi zuwa Saudiyya
- Kotu ta umarci MTN ya biya mawaki diyyar N20m
Rahotanni sun ce Alhaji Arzika, wanda dan asalin Karamar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sakkwato ne, ya tsinci kudaden ne a kafar benen otal din da suke zaune, wanda nan ne inda aka sauke alhazan Jihohin biyu.
Alhajin dai ya ce ko daya ba ya da-na-sanin mayar da kudin ga mamallakinsu.
Aminiya ta gano cewa mafi yawan kudin guzurin da ake ba maniyyata a Aikin Hajjin bana ba ya wuce Dala 850.
Daga bisani dai an kai jakar kudin zuwa ofishin Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), inda Jami’in hukumar na birnin Madina, Alhaji Ibrahim Mahmud, ya karbe su.
Da yake bayani bayan mayar da kudin, Alhaji Arzika ya ce, “Lokacin da ake yi mana bita, malamai sun nuna mana muhimmancin mayar da abin da ba naka ba musamman a Saudiyya. Duk abin da ka tsinta ya zama wajibi ka mayar da shi.
“Wannan ne ya sa ina tsintar kudin na kai wa wani jami’in Hukumar Jin-dadin Alhazai ta Jihar Sakkwato.
“A can ne ma muka gano kudin da ke cikin jakar. Sai muka yi sa’a a jikin jakar akwai lambar waya ta ta fasfo din mai ita, wacce muka gano ta wani maniyyacin Jihar Kaduna ce. Ina farin cikin cewa na yi abin da ya dace,” inji shi.
Da yake jawabi yayin bikin mayar da kudin, Jami’in na NAHCON, Alhaji Ibrahim, ya gode wa Arzika, tare da alkawarin mayar da kudin ga Hukumar Jin-dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, domin a damka su ga mai su.
Yayin bikin mika kudin dai, an yi wa alhajin da ya mayar da kudin addu’a da ma Jihar Sakkwato da Najeriya baki daya. (NAN)