Allah Ya yi wa shahararren dan kasuwar nan na Zariya, Alhaji Usman Bako Zuntu rasuwa.
Iyalan mamacin sun ce ya rasu ne da Asubahin Juma’ar nan a Asibitin Al-Madina da ke GRA a Zariya bayan ya yi fama doguwar jinya.
- Diphtheria: Abubuwan da ya kamata ku sani game da bakuwar cutar da ta kashe mutum 25 a Kano
- Duniya na cikin tsaka mai wuya —Gutteres
Alhaji Bako Zuntu wanda ta shafe shekaru 84 a doron kasa, ya kasance babban dan kwangila kuma shahararren dilan kayayyakin masarufi a Kamfanin PZ.
An haife shi a garin Zuntu na Karamar Hukumar Kubau da ke Jihar Kaduna, amma ya kasance mazaunin Unguwar Magume da ke Tudun Jakun Zariya duk tsawon rayuwarsa.
Kafin rasuwarsa Alhaji Bako Zuntu, babban manomi ne kuma attajiri da ke amfani da dukiyarsa wajen tallafa wa al’umma.
Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 26 da jikoki da dama.
Wakilinmu ya ruwaito cewa za a yi jana’izarsa a Masallacin Juma’a da ke Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, daura da Kamfanin Buga Takardu na Gaskiya, bayyan an idar da sallar Juma’a.