✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alhaji ba ka biya ni kudin wankin ba!

Wani Alhaji ne yana da mai wanki da guga da yake jin dadin aikinsa saboda ya iya aiki da gaskiya da amana. Wata rana aka…

Wani Alhaji ne yana da mai wanki da guga da yake jin dadin aikinsa saboda ya iya aiki da gaskiya da amana. Wata rana aka kai msa wankin kayan Alhaji da na matarsa da ’ya’yansa. Bayan ya wanke ya goge sai ya shiga ban-daki kafin ya fito, sai barawo ya sace kayan duka.
Hankalinsa ya tashi, karshe ya yanke shawarar ya je ya sanar da Alhaji.Yana zuwa ya fada masa abin da ya faru. Matar Alhaji ta yi ta masifa tana cewa sai ya biya. Da kyar Alhaji ya lallashe ta ya ce kada ta damu Allah Ya riga Ya kaddara ko a wajensu suke sai an sace. Sai ya ce wa mai wankin shi ke nan je ka.
Amma sai ya ga mai wanki bai tafi ba, sai ya ce za ka iya tafiya ba komai mun yafe. Budar bakin mai wanki sai ya ce, “Alhaji ai ba ka biya ni kudin wankin ba.”
Daga 09092969381