Wani babban jami’i a asibitin Memfys da ke jihar Enugu ya ce Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Dokta Alex Ekwueme na raye kuma yana kara murmurewa.
Jami’in ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Enugu a jiya cewa “Ekwueme yana asibitin Memfys da ke Enugu kodayake Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da ummarnin a kai shi kasahen wajen don samun kyakkyawar kulawa”.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa an kwantar da tsohon mataimakin shugaban kasar a asibitin sakamakon ciwon kirji.