✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Albarkar Kirsimeti (2)

Ina yi taya kowane dayanmu murna kan yadda Allah cikin ikonSa Ya yarda Ya kuma bar mu cikin masu rai da suka ga sabuwar shekara…

Ina yi taya kowane dayanmu murna kan yadda Allah cikin ikonSa Ya yarda Ya kuma bar mu cikin masu rai da suka ga sabuwar shekara ta 2014. Idan kuma nufinSa ne bari Ya sa mu gama wannan shekara cikin salama da kuma lafiya, amin.
Makon da ya gabata mun soma koyarwa ce a kan albarkar Kirsimeti, muna kan duba dalilan da suka sa Yesu Kiristi ya shigo cikin wannan duniya, muka kuma soma duba shirin halittar mutum.  
Ashe kowane mutum a fuskar duniyar nan kasa ne kawai; ko kuwa rairayi ne kawai idan ba domin numfashin rai daga wurin Ubangiji Allah ba. Bambancin mutum da dabba abu daya ne kawai, tushen rai wanda suke dauke da shi; Yayin da Allah Shi ne Mahaliccin kowa da komai, amma hanyar da Allah Ya ba wa kowace halittarsa ya bambanta. Ga sauran halitta Allah magana ne kawai Ya yi, amma da ya zo ga halitar mutum, Ya siffanta shi tukuna da turbaya, ko laka, ko kuwa kasa, bayan ya gama siffanta mutum sai ya hura masa numfashin rai daga gare Shi kafin mutum ya samu rai da ya rayu da shi a cikin gonar Adnin. Za mu iya ganewa daga wannan wuri cewa; abin da mutum ke rayuwa da shi ainihin – numfashin Allah ne, wannan ba karamin abu ba ne. Gaskiyar ita ce idan ba domin numfashin da Allah Ya ba mutum daga gare Shi ba, da mutum matacce ne ba shi da rai. shi ne ma ya sa a karshen rayuwarmu a wannan duniya, dole mai numfashin rai din nan zai karbi kayanSa, dole ne ‘ranmu’ ya tsaya a gaban Allah domin shari’a, ba wannan jiki ne zai ga Allah ba.
Wannan babu shakka, domin rai da kake dauke da shi a yau, ba naka ba ne; mai shi yana da iko da kuma ’yanci ya dauki kayansa ko yanzun nan ma idan ya ga dama, Wannan rai amana ne daga wurin Allah, komai ilimin kimiyya babu wanda ya iya ‘kera’ rai kuma babu wanda zai iya yi.
Lokacin da Allah Ya halici mutum, Ya ba shi dukkan abin da zai bukata cikin dukan rayuwarsa; ba zai taba zama da babu ba; komai da yake bukata a yalwace suke a ko’ina cikin gonar Adnin. Allah Ya riga Ya shirya masa cikakken rayuwa cikin ni’ima da jin dadi cikin wannan gonar. Allah Ya damka a cikin hannun mutum shugabancin dukan abin da Shi Allah Ya halitta, duk wannan kafin mutum ya yi zunubi ne. Shigowar zunubi cikin duniya ne ya canja duk kyakkyawan shiri da Allah Ya yi domin mutum. Kafin wannan zunubi, Allah Yakan sauko Ya ziyarci mutum, su yi magana, ya zamana cewa; yayin da Allah Yana mulki bisa komai da kowa wato abin da cikin sammai da dukan abin da ke bisa doron duniya; sai ya ba mutum ’yancin yin mulki bisa duk abin da Shi Allah Ya halita a wannan duniya.
Zunubi ya shigo duniya ne ta wurin rashin biyayyar Adamu da Hauwa’u. Allah Ya riga Ya ba su umarni game da yadda za su yi rayuwarsu cikin gonar Adnin, Ya ba su kashedi a bisa itacen da ke cikin gona da ba za su ci daga cikin ’ya’yansa ba, su kuma, sai su ka bar Shaidan, Iblis ya rude su har suka ci daga cikin ’ya’yan itacen nan cikin rashin biyayya. Wannan rashin biyayyar ne ya zama sanadin korarsu daga cikin gonan nan mai ni’ima zuwa cikin daji kawai domin su nemi abincin kansu. A cikin sura uku na Littafin Farawa daga aya ta fari, maganar Allah ta ba mu cikakken bayani game da abin da ya faru kamar haka: “Amma maciji ya fi kowace dabbar da Ubangiji Allah Ya halita hila. Ya fa ce wa macen, ashe ko Allah Ya ce, Ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba? Sai macen ta ce wa macijin, daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mana mu ci: amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona, Allah Ya ce, Ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taba ba domin kada ku mutu. Sai Macijin ya ce wa macen, Ba lallai za ku mutu ba: gama Allah Ya sani ranar da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta. Sa’anda macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin ba da hikima, sai ta debi ’ya’yansa ta ci, ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci.
Dukansu biyu kuwa idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su; suka dundunke ganyayen baure, suka yi wa kansu mukuru. Sai suka ji muryar Ubangiji Allah Yana yawo cikin gona da sanyin yamma: mutumin fa da matarsa suka buya daga fuskar Ubangiji Allah a cikin itatuwan gona. Ubangiji Allah kuma Ya kira mutumin Ya ce masa, ina kake? Shi kuwa ya ce, Na ji motsinka cikin gona, na ji tsoro, domin tsirara nake: na kuwa buya. Ya ce masa, wa ya fada maka tsirara kake? Ko ka ci daga itace, wanda na dokace ka da ka ci? Mutumin ya ce, macen da ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci. Sai Ubangiji Ya ce wa macen, mene ne wannan da kin yi? Macen ta ce macijin ne ya rude ni, ni kuwa na ci. Ubangiji Allah Ya ce wa Macijin, tunda ka yi wannan, la’ananne ne kai cikin dukan bisashe da kowane dabba; rub-da-ciki za ka yi tafiya, za ka ci turbaya kuma dukan muddar ranka: tsakaninka da mutumin kuma zan kafa magabtaka da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya kuje kanka, kai kuma za ka kuje duddugensa.