✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Albarkar Kirsimeti (1)

Kirsimeti lokaci ne da dukan Kirista cikin duniya gaba daya sukan dauki lokaci su tuna da ranar ‘Haihuwar’ Yesu Kiristi a cikin wannan duniya, lokacin…

Kirsimeti lokaci ne da dukan Kirista cikin duniya gaba daya sukan dauki lokaci su tuna da ranar ‘Haihuwar’ Yesu Kiristi a cikin wannan duniya, lokacin murna ne sosai; musamman ma idan muka tuna da ainihin dalilin shigowarsa cikin wannan duniya, wanda shi ne ceton dan Adam duniya daga halaka tare da Iblis a ranar karshe. Ina so mu duba labarin shigowar Yesu Kiristi cikin wannan duniya. “Ana nan cikin wata na shidda aka aiko mala’ika Jibra’ila daga wurin Allah zuwa wani birni na Galilee, sunansa Nazarat, zuwa wurin wata budurwa da wani namiji yana tashinta, sunansa Yusufu ne, na gidan Dauda; sunan budurwa kuma Maryamu ne. Mala’ika ya shiga wurinta, ya ce, a gaishe ki, ke da kike mai samun alheri, Ubangiji Yana tare da ke. Amma hankalinta ya tashi kwarai da zancen, ta yi zullumi kuwa a ranta kowace irin gaisuwa ce wannan. Mala’ika ya ce mata, kada ki ji tsoro Maryamu, gama kin samu tagomashi wurin Allah. Ga shi kuwa za ki yi ciki, za ki haifi da, za ki ba shi suna YESU. Shi za ya zama mai girma, za a ce da shi dan Madaukaki: Ubangiji Allah kuma zai ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za ya yi mulki kuma bisa gidan Yakub har abada; mulkinsa kuma ba ya da matuka. Maryamu ta ce wa mala’ika, yaya wannan zai zama, da yake ban san namiji ba? Mala’ika ya amsa ya ce mata: Ruhu Mai tsarki za ya auko miki, ikon Madaukaki kuma za ya inuwantar da ke: domin wannan kuwa abin da za ki haifa, za a ce da shi mai tsarki dan Allah. Ga kuwa Alisabatu danginka, ita kuma da tsufarta tana da da a cikinta: wannan kuwa shi ne wata na shida gare ta, ita wadda aka ce mata bakarariya. Gama babu magana daga wurin Allah da za ta rasa iko.”(Luka:1: 26–38).
Dukan wannan cikar annabcin da aka yi ne shekaru da dama da suka gabata; wato tun zamanin Annabawa ke nan; a cikin Littafin Annabi Ishaya 8: 20–9: 7, maganar Allah na koya mana cewa “A komo bisa ga shari’a da Shaidan! Idan ba su fadi bisa ga wannan magana ba, hakika babu wayewar gari a gare su ba. Za su ratsa ta cikinta, da kyar da yunwa kuma: za ya zama kuma, lokacin da suke jin yunwa, za su damu ransu, su la’anta Sarkinsu da Allahnsu, su maida fuskarsa a wajen sama: za su duba wajen kasa, su ga wahala da duhuwa, duhu bakin kirin na azaba ke nan: za a kore su kuma cikin bakin duhu.
Amma ba za a yi duhu wurinta wadda take cikin azaba a da ba. Cikin kwanakin da ya maida kasar Zebulun da kasar Naphtali abin raini; amma cikin kwanaki na karshe ya darajanta ta, ta hanyar teku, ketaren Urdun, Galilee na al’ummai. Mutanen da ke tafiya cikin duhu sun ga haske mai girma; mazauni cikin kasa ta inuwar mutuwa, a bisansu haske ya bullo. Ka yawaita al’ummar, ka kara musu farin ciki: suna murna a gabanka irin murna ta kaka, kamar yadda mutane suke murna sa’adda suke rarraba ganima. Gama ka karya kangi na kayansa da sanda ta kafadarsa, keren mai yi masa wulakanci, kamar cikin ranar Midiyan. Gama dukan kayan mayaki cikin rigimar yaki da tufafi mirginannu cikin jini, za su zama na konewa, abincin wuta.
Gama an haifa mana yaro, a gare mu an bada da, mulkin za ya kasance a kafadarsa: za a ce da sunansa al’ajibi, Mai shawara, Allah Mai iko duka, Uba Madauwami, Sarkin Salama. karuwar mulkinsa da salama ba ta da iyaka, a bisa kursiyin Dawuda da bisa mulkinsa, domin a kafa shi, a tabbatar da shi ta wurin gaskiya da adalci daga nan gaba kuma har abada. Himmar Ubangiji mai runduna za ya aikata wannan.”
Ina so mu soma duba dalilin da ya sa Yesu Kiristi ya shigo cikin wannan duniya. Abu na farko shi ne; lokacin da Allah Ya halici mutum tun farko, Ya yi ne domin Ya cika nufinSa a cikin wannan duniya, a cikin Littafin Farawa:1: 26–31; maganar Allah na koya mana cewa “Kuma Allah Ya ce, bari Mu yi mutum cikin surarMu, bisa ga kamanninMu: su yi mulki kuma bisa kifaye na teku da tsuntsaye na sama da bisashe da kuma bisa dukan duniya da kowane abu mai rarrafe wanda ke rarrafe a bisa kasa. Allah fa Ya halita mutum cikin sura taSa, cikin surar Allah Ya halice su, namiji da ta-mata Ya halice su. Allah Ya albarkace su kuma: Allah Ya ce musu, ku yalwata da ’ya’ya, ku ribanya, ku mamaye duniya, ku mallake ta; ku yi mulkin kifaye na teku da tsuntsaye na sarari da kowane abu mai rai wanda ke rarrafe a kasa. Allah kuma Ya ce, Ga shi na ba da kowane ganye mai ba da kwaya da ke bisa fuskar duniya duka da kowane itace, wanda ’ya’yan itace mai ba da kwaya suna cikinsa ya zama abincinku; kuma na ba da kowane ganye ga kowane dabba na duniya da kowane tsuntsu na sama da kowane abin da ke rarrafe a kasa wanda rai ke cikinsa ya zama abincinsu; haka kuwa ya zama. Allah kuma Ya duba kowane abin da Ya yi, ga shi kuwa yana da kyau kwarai. Akwai maraice akwai safiya kuma, kwana na shida ke nan.”
To lallai idan har muna so mu gane dalilin zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya, dole ne mu sake duba dalilin da ya sa Allah Ya halicci mutum. Abu na farko dai shi ne; a cikin dukan halittar da Allah Ya yi babu wani abu guda daya da ya sa hannu ya cura shi da ko ma mene ne, sai mutum shi ka daii, sauran halitta duka Allah cikin ikonSa Ya fadi ne kawai, sai duk abin da Ya fada ya kasance dai kamar yadda Yake so; mutum kadai ne Allah Ya dauki lokaci Ya shirya halittarsa kamar yadda muka gani a cikin Littafin Farawa:2:7, wadda take cewa “Ubangiji Allah kuwa Ya siffanta daga turbayar kasa, Ya hura masa numfashin rai cikin hancinsa; mutum kuwa ya zama rayayyen mai rai.”
 
Za mu ci gaba da bayani mako mai zuwa idan Allah Ya yarda. Salama!!