Alhaji Musa Sakkwato shi ne shugaban masu sayar da kayan gwari a Kasuwar Randa. dan kasuwar wanda ya dade yana aikace-aikacen kungiyoyin al’ummar Arewa mazauna Jihar Ogun, ya shaida wa Aminiya irin alfanun da suka samu a dalilin kafa kungiya. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Musa Sakkwato: Sunana Musa Sakkwato, ina zaune ne a garin Sabo Abeoukuta, ni ne shugaban masu sayar da kayan gwari a Kasuwar Randa, kuma uban kungiyar hadin kan mutanen Arewa a jihar nan.
Aminiya: An ce kungiyarku ta takaita ne da Sakkwatawa da Zamfarawa da kuma Kabawa, ko gaskiya ne?
Musa Sakkwato: Eh da farko haka abin yake sai daga bisani muka ga ya dace mu hade kawunan mu wato ’yan arewa mazauna kurmi baki daya. Duk wani dan arewa da ya tsallako daga gadar Jaba to yana ciki, da ba ka ne da Bafullace da Babarbare kai har da dan Nijar matukar ya zauna a cikinmu na tsawon wasu shekaru to duk mun zama guda ke nan.
Aminiya: Ko me ya ja hankalinka kake kafa kungiyoyi?
Musa Sakkwato: To Alhamdulillahi na gode wa Allah da kazo ka sameni cikin koshin lafiya har kai mini wannan tambayar, ni mutumne mai san mutane su yi hulda da ’yan uwansu ko wanne ya gane dan uwa nai to wannan ya sa daga ina wannan ya fito, albarkacin kungiyarnan, ko abu ne ya same ka idan dan kungiyarka ya ganka ko Bahaushe ne ko Tibi ne kai koma waye zai dakata ya ce wannan dan kungiyarmu ne.
Idan abin da zai iya kaima dauki ne ya yi, idan wanda za a sanar da shugabannin kungiya ne sai ya sanar musu su kawo masa dauki. Duk lokacin da dan kungiyarmu ya shiga matsala idan abin sulhuntawa ne muje mu sulhunta, domin babar manufarmu ita ce zaman lafiya kuma mun gode Allah mu da abokan zamanmu Yarbawa muna zaune lafiya suna da biyayya mu ma haka muke binsu sannu a hankali.
Aminiya: Wane irin alfanu kuka samu daga kungiya?
Musa Sakkwato: Hakika mun sami amfani duk wanda muka ga bashi da abinci ko ya shiga wani hali, sai mu kirawo taro mu ce kowa ya saka tasa gudunmawa, mai naira 500, mai 100 mu tara kudin mu taimaka masa a dalilin kungiya.
Akwai wani lokaci da wani mutum Bayarbe ya ba mu kasuwa a can hanyar Jihar Legas. Yadda al’amarin ya faru shi ne wata rana, muna taro sai ya tambaye mu “me kuke yi haka”?
Muka ce taron kungiya ne sai abin ya burge shi ya ce mana mu zo akwai filin da ya gada a wurin mahaifinsa ya ba mu mu yi kasuwa a wajen haka kuma aka yi, ya ce mana a Sabo aka haifeshi iyayensa sun zauna lafiya da mutanen Arewa. Ka ga mu a nan Abeokuta ba a taba samun rikici a tsakanin Hausawa da Yarbawa ba.