A ranar Juma’ar da ta gabata ce Kotun daukaka kara da ke Legas ta warware hukuncin kisa da wata Kotun Majistare ta yanke wa Manjo Hamza Al-Mustapha da Alhaji Lateef Shofolahan kuma ta wanke su kan zargin kashe Cif Kudirat Abiola, matar marigayi Mashahood Abiola. Wakilinmu ya tattauna da Manjo Hamza Al-Mustapha da Alhaji Lateef Sofolahan kan lamarin:
An yanke maka hukuncin kisa da aka ci gaba da shari’a sai kuma aka yanke hukunci ba ka da laifi, kotu ta sallame ka, shin yaya ka ji a wadannan lokuta biyu?
Na farko, wato lokacin da aka yanke mini hukuncin kisa, su kansu lauyoyin Legas sun ce ba mu da hujjoji a rubuce, amma dai muna so a kama Al-Mustapha saboda ya yi aiki da marigayi Janar Sani Abacha, saboda shi ya lura da Janar Abacha shi kuma ya mulki kasar nan, wannan shi ne kawai laifina. Amma abin mamaki sai a ce an yanke wa wanda ya aikata hakan hukuncin kisa. Shi ya sa ko ranar da aka yanke mini hukuncin kisa ban damu ba, saboda ba na shakkar irin wadannan mutane, a duba na yi aikin soja, wadanda muka shiga soja da su da yawansu sun mutu, amma ni da raina, shin na fi su ne? Ban fi su ba, amma a ce ina soja kuma ina shakka ko kuma tsoron mutawa. A wannan ranar na rika ba mutane hakuri, har na ce idan Fir’auna ya isa to ya dawo, magana ce babba idan kun fahimta. Ma’anar hakan ita ce, duk wanda ya dauka cewa shi ya isa, ba Allah ke da mulki ba, to ka ji tausayin wannan mutum, domin ko wane ne shi lokacinsa zai kare, kuma ko wane ne shi bai yi irin na Fir’auna ba. To tunda Fir’auna ya gushe ashe babu wanda zai rage. Duk wanda ya dogara ga Allah ai ya gama.
Dangane da ranar da aka sake ni kuma sai na yi wa Allah godiya. Duk wanda ya kyautata dangartakarsa da Ubangiji, ba zai tabe ba. Kuma Allah Ya yi alkawarin duk wanda ya mayar da al’amuransa gare Shi, to zai iya masa.
Ana zarginka da tsauri, shin haka ne?
An ce ina da irin hali na masu tsattsauran rai, a’a ba haka ba ne. Ni dai ina da wani abu, in dai a kan hakkin mutane ne, ko kuma batun kare Najeriya, to zan kare koda kuwa za a ba ni baitul-malin duniya ba zan karba don na bari a cutar da kasata ba, ban yi haka ba, kuma ba zan yi ba, domin wannan halinmu ke nan. A wurin wadansu kuma wannan halin abin tsoro ne, to kuwa ba za mu taba canzawa ba.
Abubuwa da yawa sun faru gare ka na farin ciki da bakin ciki, shin ko akwai wani abu da ka aikata wanda a halin yanzu kake nadama?
Ba na maganar da-na-sani, ba na kuma maganar nadama. Na daya abubuwan da za a ce na yi nadama a kai, to kage aka yi mini, cewa ba ma son mutane, mu masu musguna wa mutane ne ba haka ba ne. Duk wanda ya san lokacin da muke aiki, bari na ba da misali a Abuja, wato a lokacin Janar Abacha yana Shugaban kasa, karfe 6:00 na safe nake barin ofis. Ma’ana a ofis muke kwana, ko kuma a kan titi don samar da tsaro. Hakan ya sanya muka san abubuwan da suke faruwa a kasar nan. Ba a kara mini albashi ba, ba wani alawus aka ba ni ba, ba kuma wani ne yake daukar wani kudi yake ba ni ba, ko Janar Abacha bai daukar kudi ya ba ni, na dauki duk wani aiki da za ka yi na kare kasa a matsayin bauta ga Ubangiji.
Ka ce ba ka fata ko makiyinka ya je fursuna. Kai da Shofalan ba ku yi kama da wadanda suka shiga fursuna ba, mene ne sirrin wannan al’amari?
Duk mutumin da aka sanya shi a fursuna tamkar mutumin da aka jefa shi a cikin teku ne, idan ka ce za ka yi ta iyo ne har ka fitar da kanka, to, za ka wahalar da kanka ne, a karshe ka kashe kanka a banza. Abin da ake so shi ne ka zauna, ka jira, amma dai kada ka yarda ka nutse a ruwa, sai dai ka rika bin igiyar ruwa, idan ta kai ka wani tsibiri, to daga nan ne za ka fara tunanin inda ka nufa, don haka idan ka ga wani abu ya faru da kai sai ka bar wa Allah, kuma ka yi amfani da wurin wajen bauta wa Ubangiji cikin kwanciyar hankali. Wata hikima da na yi a lokacin da nake fursuna ita ce, na mayar da kaina kamar wani dan makarantar sakandare, ina da wani jadawali (time table), inda nake tashi daga karfe 1:00 na dare na rika ibada, wato na rika salloli da karatun kur’ani da kuma addu’o’i. Wani lokaci na rika tunani da kuma rubuce-rubuce har takwas na safe. Daga takwas kuma zan yi barci zuwa goma. Daga karfe goma kuma zan je na ga bakin da aka bari su gan mu, a lokacin da zan dawo Azahar ta yi. Zan zauna a masallaci har zuwa Sallar La’asar, daga La’asar zuwa Magariba akan yi guje-guje, ba na wasa da wannan. Har nakan matsa wa wadanda muke tare su rika motsa jiki, duk wani abin wasa da na samu a fursuna na inganta su, na kuma tilasta wa mutane su yi, saboda su samu lafiya, kada su mutu a banza. Mutane sun mutu saboda rashin motsa jiki, kamar Alhaji Ammana Tijjani mutumin kasar Nijar, yanzu haka yana fama da shanyewar jiki sakamakon damuwa. Motsa jiki da kuma tawakkali ne ya sanya ba ku ga damuwa ko wani hali a tare da mu ba.
Yanzu ga shi ka baro fursuna kuma ka gina masallaci, shin bayan hankalinka ya kwanta ko akwai wani abu muhimmi da za ka ci gaba da yi wa fursunoni?
Wannan babu shakka na gina masallatai biyu, sannan na yi makarantar karatun kur’ani, ina kuma biyan limamai da masu yi musu tafsiri albashi duk Juma’a. Na kuma shirya hikimar yadda za mu rika sayen abinci a cikin kudin da ya rage mini ana ba wadanda ba su da shi, ko yanzu a cikin azumin nan kafin na baro can sai da na sayi abinci aka raba. Duk tsawon shekara 15 din nan haka nake yi. Babu wanda ya sa ni, na yi ne saboda da Allah. Zan kuma ci gaba, ba ma ni kadai ba zan koya wa abokaina yin sadaka tagari, su kuma fahimci talaka na da girman gaske a wurin Ubangiji.
Ko akwai wani abu da kake so mutane su sani?
Kun san aikin tsaro nake yi, idan na fara fada muku wani abu da nake so mutane su sani, to, sai na tayar da wata guguwar da watakila ni da ku ba za mu iya magance ta ba. Gara a bari haka.
Allah Ya karbi addu’ata
– Kakar Al-Mustapha
Daga Isa Muhammad Inuwa, Kano
Kakar tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha da ake kira Hajiya Babba, ta ce Allah ne Ya amshi addu’arta aka sake shi, kan zargin kashe Kudirat Abiola da Kotun daukaka kara da ke Legas ta yi. Ta ce addu’a ce maganin komai, don babu abin da ya gagari addu’a. Ta gode wa duk wadanda suka taimaka wajen wanke Al-Mustapha daga wannan zargi. “Ina godiya ga Ubangiji da Ya amshi addu’ata,” Ta ce tun farkon kama Al-Mustapha take ta addu’a ba dare ba rana, don ganin an sake shi.
Hajiya Babba wadda ke kan katifarta, saboda raunin jikinta kuma take amfani da keken guragu, yayin zama ko tafiya, an ce ta haura shekaru dari a duniya.
’Yan uwana sun guje ni yayin da nake jarun
– Sofolahan
Daga Abubakar Ibrahim, Legas
Aminiya: Tunda kun san wadanda suka sanya ku a wannan hali me za ka yi a kai?
Sofolahan: Da farko dai na gode wa Ubangiji da Ya sa na ga wannan rana. Ba domin yardar Allah ba, sannan da kokarin Manjo Al-Mustapha da yanzu ba zan san inda nake ba. Misali wata rana Al-Mustapha ya yi rashin lafiya aka kai shi asibiti, sai bai son fita waje, sai na je asibiti na same shi na ce, “Ina son ka san cewa da ka mutu gwamma ni na mutu.” Dalili idan Al-Mustapha ya mutu, ba wanda zai taimaki ’ya’yana, amma idan na mutu Al-Mustapha zai taimaki yarana. Saboda haka abin da ya faru da mu, mun yarda da Allah ne Ya hukunta. Idan ka dube ni yanzu mutum ba zai ce maka na fito ne daga kurkuku ba. A kan wadanda suka dora mana wannan laifi, suka ce mu ne muka yi, na gode wa Ubangiji da Ya kubutar da mu. Allah Ya sani ban taba aiki da Hajiya Kudirat Abiola ba, Allah Ya jikanta. Ana ta surutai iri-iri, a ce Shofolahan ne PA dinta, shi ne direbanta, shi ne mai dafa mata abinci. Sau da yawa na sha fada a kotu cewa, ‘don Allah DPP ko IPO ku kai ni gidan Abiola a nuna ni, domin in ji wanda zai ce ina aiki a gidan. Bba na aiki a gidan Abiola, don haka wadanda suka yi mini kazafi na bar su da Allah Shi ne zai saka mini duniya da Lahira.
Aminiya: Kafin aukuwar wannan abu a gare ku, wace sana’a kake yi?
Sofolahan: Ina sayar da lemon kwalba ne, sunan shagona September 10 Enterprises, yana lamba 12 Itire Road, Abeokuta Bus Stop, ina karbar lemon kwalba daga kamfanin koka-kola.
Aminiya: To yaya aka yi aka sawo ka cikin maganar?
Sofolahan: Yadda aka kawo ni cikin maganar shi ne, na yi aiki da kwamitin kamfe din Abiola mai suna HOPE ’93. Bayan an rushe zaben, sai aka kore mu daga HOPE ’93, kuma mai gidana a lokacin shi ne Dokta Jonathan Zwingina, ko yau aka kira shi, ba zai ce na yi aiki a gidan Abiola ba.
Aminiya: Da kuka shiga wannan matsala Dokta Zwingina bai ce ba ka da hannu a abin da ake tuhumarka ba?
Sofolahan: Ka san dan Adam da halinsa, kuma ga mutum mai neman mulki dan siyasa. Sannan ban kira shi ba, gwamnati ma ba ta kira shi ba, kai a lokacin ban san inda yake ba, balle in aika masa. Sannan idan ya sa baki a maganar kila Yarabawa su ji haushinsa cewa bai fadi gaskiya ba. Ka san mutanen duniya yau ba a son gaskiya, amma wallahi tallahi ban taba aiki a gidan Abiola ba.
Aminiya: Me kake ji ya sa aka lankayo ka a cikin batun, alhali ba kai kadai ka yi aiki a Hope ’93 ba?
Sofolahan: Abin da ya sa aka sa ni cikin wannan batu, bari in kai ka yadda har na san Hajiya Kudirat Abiola. Lokacin ina jami’in kula da baki a HOPE ’93, an ba ni dawainiyar kula da dakuna a otel din Gateway mai dakuna 222. Ni ke kula da duk dakunan, kuma Cif Abiola ya ba
Ta dawainiyar kula da duk matan Arewa, Hajiya Bisi kuma aka ba ta kula da kasar Yarbawa, Madam Doyin aka ba ta kula da kasar Ibo. Wadannan mata suna aiko min da takarda cewa in ba su dakuna biyar, wasu in ba su daki uku, idan na ki bayarwa, sai su rubuto min wasika cewa in zo in same su, to ka ji ta yadda har na taba shiga gidan Abiola.
Aminiya: Shin za ku yafe wa gwamnatin Jihar Legas wadda ta kai kararku aka tsare ku na tsawon shekara 14?
Sofolahan: Duk abin da Al-Mustapha ya ce shi zan bi, saboda gaskiya Al-Mustapha ya taimake ni, domin duk kudin da lauyoyi ke karba shi ne ke biya. Yarbawa ’yan uwana sun guje ni, hatta wadanda muke uwa daya uba daya sun guje ni. Ban ji dadi ba, wadda take bi na Kemi da Funlola da Bola da Gbenga, wallahi duk ban ji dadinsu ba, sun ki ni.
Aminiya: Ga shi ka fito, yaya dangantaka tsakaninka da su za ta kasance?
Sofolahan: Da suka ji cewa an sake ni, sai suka fara kirana suna cewa dan uwa kaza-kaza, muna murna, ka san munafuncin Yarbawa yadda yake.
Aminiya: Kana nufin sa’ilin da kake tsare ba mai zuwa wurinka cikin ’yan uwan naka?
Sofolahan: Tun lokacin da aka kama ni a 1999, wadda take bi na ta zo kurkuku sau biyu, kuma tun lokacin da aka ce an yanke hukuncin za a kashe mu ba wanda ya taba zuwa wurina a cikinsu.
Aminiya: Ina matarka da ’ya’yanka?
Sofolahan: Ka san ni Bayarabe ne mai son mata da yawa, na auri mata bakwai da na haifi ’ya’ya da su, kafin a kama ni ina da mata uku cikin gidana. To, bayan an kama ni, suka ga cewa shekara daya, biyu, uku, ban dawo ba, sai suka gudu. Ka san Yarbawa ba su da hakuri kamar Hausawa. Misali ga Aminu ya samu shekara 12 a tsare amma matarsa ba ta gudu ba, ga Hajiya namu nan da yaranta, to ina za ta je.
Aminiya: To kai ina yaranka suke?
Sofolahan: Yarana suna nan, yanzu haka akwai mai tallar burodi. Yanzu ba ni da komai an kone gidana. Mohammed Abacha da Alhaji Nasiru yayan Manjo Al-Mustapha sun san an kone gidana lokacin da aka kama ni a 1999, ba ni da gida ina zan koma yanzu?
Aminiya: To da aka sako ku shekaranjiya ina ka je?
Sofolahan: Al-Mustapha yana daga kafa, sai ka ga kafata a wurin. Shi zan bi har karshen rayuwata. Ko ya koma soja, ko a yi masa karin girma, saboda shi mai taimakon jama’a ne, kuma mun sha wuya tare da shi, duk inda ya ce in zauna nan zan zauna, shekarata 66, kwana nawa ya rage min a duniya in mutu?
Aminiya: Yaya rayuwa ta kasance muku a gidan yari?
Sofolahan: Ai ba a magana, gidan yari ba wurin da ake jin dadi ba ne, katanga guda hudu, kana ciki shekara 14, wanda a da kana da gadon kwana kafa bakwai, sai ga shi ka je wurin da za a auna tsawon takalmi shi ne wurin kwananka.
Aminiya: Amma ba ka yi kama da wanda ya zauna a kurkuku ba?
Sofolahan: To na gode Allah, da ka ga na zama bulbul aikin Al-Mustapha ne da Alhaji Nasiru da Fani Amu. Harshe da hakori suna sabawa ba yadda ni da Mustapha ba za mu samu rashin fahimtar juna ba. Muna samun rashin fahimtar juna a tsakaninmu, na sha yi masa laifi, amma da Fani Amu ya yi masa magana shi ke nan ya manta. Domin da haka ta faru sai in fada wa Fani Amu cewa Ambassada na yi wa maigidana laifi.
Aminiya: Ga shi iyalan gidan wadanda ake zargin kun kashe na cewa ba su gamsu da hukuncin da ya sallame ku ba, me za ka ce game da hakan?
Sofolahan: Idan kana biye da maganar ka san ba gaskiya cikinta ko kadan, shaidar gwamnati da za a kawo kotu ya fada wa Alkali Mojisola Dada cewa ga abin da gwamnati ta ce in fadi. Misali Roggers ya shaida wa kotu cewa an saya masa gida a Ilori da Jos, inda akwai gaskiya yadda suka ce an ba su kudi, kuma an ce ga abin da za su fada, ba za a yarda da shaidarsu ba. Na biyu wata rana Roggers ya zo kotu ya shaida wa kotu cewa ku da kuka kawo ni daga Abuja wato SSS ga abin da kuka ce in fadi, ku kuma da muka tarar a nan Legas wato ofishin DPP ga abin da kuka ce in fada. Cikinsu wanne zan fada? Sai lauya ya ce masa fadi duk wanda ka ga dama, to idan ka dubi wadannan abubuwa duk cikinsu ba gaskiya.