✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al-Makura ba zai kakaba wa al’ummar Nasarawa A.A. Sule ba – Sanata danboyi

A ranar Talatar da ta gabata ce ayarin yakin neman zaben Injiniya A.A. Sule, a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APC…

A ranar Talatar da ta gabata ce ayarin yakin neman zaben Injiniya A.A. Sule, a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APC ya kira taron manema labarai a Abuja, inda ya musanta zargin da wadansu ’yan takarar Gwamnan jihar suka yi na cewa Gwamna Al-Makura na shirin sauya sunayen masu kada kuri’a a zaben fid-da-gwani da ke tafe.

“Wani rahoto da jaridar The Sun ta ranar Lahadi ta wallafa a shafinta na 40 mai taken; ’Yan takarar Gwamna a Nasarawa sun yi barazanar ficewa daga APC idan aka kakaba musu dan takara’ ya ja hankalinmu sosai,” inji A Shugaban ayarin yakin neman zaben AA Sule, Sanata John danboyi.

Ya kara da cewa, “Muna son al’umma ta san cewa wannan rahoto da jaridar ta buga ba komai ba ne face makarkashiya da yunkurin bata wa Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura suna da kuma yunkurin jefa jagorancin APC a Nasarawa cikin rudani.”

“Wadancan ’yan takara da idanunsu ke rufe, su ke jefa irin wannan zargi marar tushe ba tare da tantance yadda lamarin yake daga shugabannin Jam’iyyar APC ba, suna kokarin nade tabarmar kunyarsu ce saboda rashin tasiri da karbuwarsu ga al’ummar Nasarawa a zaben fid-da- gwanin da za a yi. In ba haka ba ta yaya wani zai fito ya yi zargin cewa an sauya sunayen wakilan da masu zaben fid-da-gwani?” Shugaban ya ce ana so ne a bata tafiyar dan takararsu Injiya A.A. Sule wanda yake samu karbuwa daga dukan al’ummar Jihar Nasarawa, kuma suka yarda shi ne jagoran da zai kai su ga gaci a jihar.

Ya ce “Da wannan ne muke sanar da al’umma cewa babu wani yunkuri na kakaba wa al’umma wanda ba su so ko kuma yunkurin sauya masu zaben ’yan takara. Jam’iyyarmu ta APC a karkashin jagorancin Gwamna Al-Makura tana nan daram tana tafiyar da ayyukanta ba tare da wani rudani ba kamar yadda masu zargin suke yi.”

“Har ila yau muna sanar da al’umma cewa Gwamna Al-Makura tare da jagororin Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa za su bai wa kowa damar shiga kowace takara a kowane mukami ta hanyar zabe na gaskiya a yayin gudanar da zaben fid-da- gwanin, duk wanda Allah Ya bai wa sai a mara masa baya,” inji shi.

Ya ce laifin Gwamna Al-Makura ga masu zargin shi ne saboda ya ce ya kamata a wannan karon a bai wa yankin da bai taba fitar da Gwamna ba a Jihar Nasarawa shi ma ya taba, kuma yankin da bai taba yi ba, shi ne Nasarawa ta Arewa, kuma wannan shi ne abin da ake nema daga kowane jagora nagari.