Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai yuwuwar kasashen Najeriya da Yemen da Sudan ta Kudu su fuskanci matsalar fari a ’yan watanni masu zuwa.
Ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoton hadin gwiwa da hukumominta guda biyu, Hukumar Kula da Abinci (WFP) da kuma Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar (FAO), suka fitar ranar Talata.
A cewarsu, la’akari da matsalar karancin abinci, mawuyacin hali, rikice-rikice, matsin tattalin arziki da sauyin yanayi, akwai bukatar a gaggauta daukar matakin kare aukuwar yunwar a kasashen da abin ya shafa.
Kasashen guda uku, inji rahoton na daga cikin wurare 20 da suka fi fuskantar tsananin matsalar abinci a duniya, kuma harsashen ya ce zai iya tabarbarewa nan da watan Yuli mai zuwa.
Kazalika, rahoton ya ambato wasu kasashen da suma suke cikin barazanar fuskantar matsalar, ciki har da Afghanistan da Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Habasha daHaiti.
Sauran kasashen sun hada da Honduras da Najeriya da Sudan da Syria da kuma Zimbabwe.
Bugu da kari, rahoton ya yi harsashen cewa a Arewacin Najeriya kawai, yawan mutanen da za su iya fuskantar karancin abincin zai iya rubanyawa har sau biyu zuwa kimanin miliyan daya da dubu 200 nan da watan Agustan 2021.
Hakan a cewarsu na da nasaba da matsalar tsaron da ta addabi yankin da kuma kalubalen tsaro wanda annobar COVID-19 ta kara ta’azzarawa.