✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar yawan talakawan Najeriya ya kai miliyan 250 a nan gaba – MDD

Majalisar ta bayyana abubuwan da gwamnati za ta yi don magance hakan

Asusun Kula da Yawan Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) ya yi hasashen cewa mutum miliyan 250 na iya fadawa kangin talauci a Najeriya nan da ’yan shekaru masu zuwa.

A makon da ya gabata ne Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar da sabbin alkaluman da suka nuna yawan matalauta a Najeriya a yanzu ya haura miliyan 133.

Sai dai a cewar UNFPA, akwai yiwuwar adadin ya kai miliyan 250 nan da wasu shekaru matukar Gwamnatin kasar ba ta mayar da hankali kan bangarorin lafiya da ilimi ba.

Wakiliyar asusun a Najeriya, Ulla Muella ce ta bayyana hakan jiya a Abuja, yayin wani taro tattaunawa kan karuwar yawan jama’a a Najeriya.

A cewarta, “Yana da matukar muhimmanci mu dauki matakin da ya dace yanzu, a duniyar da take da mutum biliyan takwas, a kasar da saura wasu ’yan shekaru ta zama ta uku a yawan jama’a a duniya, mutum miliyan 250 za su iya rayuwa cikin walwala.

“Amma muddin ba a yi abin da ya dace ba, akwai yiwuwar wannan adadin su kasance cikin kangin talauci da matsalar tsaro.

“Dole mu tashi tsaye wajen daukar matakai irin su tsarin iyali,” inji jami’ar asusun.

Shi kuwa da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Nasir Isa Kwarra, ya ce tsara yawan jama’a abu ne da yake bukatar tsari matuka.

Sai dai ya ce, “Hakan na bukatar kowacce kasa ta cika wasu sharuda da za su rage yawan haihuwa don tsara manufofin tattalin arziki.”