✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai yiwuwar Sunday Igboho ya ci gaba da zama a Kwatano har Buhari ya bar mulki

An bayar da belin nasa ne bisa sharadin ba zai bar Kwatanon ba, kan kowane irin dalili.

A ranar Litinin ne gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki mutumin nan mai fafutukar kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

An sake shi ne a domin ya samu damar zuwa asibiti a duba lafiyarsa, amma a cikin kasar, bayan ya shafe kwana 231 a tsare a wani gidan yari a Kwatano, babban birnin kasar.

Sai dai lauyan Igbohon, Yomi Aliyu, SAN, ya shaida wa jaridar Punch cewa wanda yake karewar ba zai iya barin kasar ba, duk kuwa da bayar da belin nasa da kotun ta yi.

A cewarsa, an bayar da belin nasa ne bisa sharadin ba zai bar Kwatanon ba, kan kowane irin dalili.

“Hakika an saki Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ga likitoci bisa yarjejeniyar cewa ba zai fice daga kasar ba bisa kowane dalili.

“Dole ne a yaba wa wasu fitattun Yarabawa biyu; Farfesa Wale Adeniran da Farfesa Banji Akintoye, saboda gudunmawarsu a lamarin,” inji lauyan.

Sai dai jaridar ta kuma rawaito cewa akwai yiwuwar Igbohon ya ci gaba da zama a Kwatanon har zuwa watan Mayun 2023, lokacin da wa’adin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kare.

An dai damka shi ne a hannun Farfesa Wale Adeniran bayan sakin nashi.

Banji Akintoye, wanda tun da farko shi ne ya tafi Jamhuriyar Benin don kwato Igbohon, ya bayyana sakin nasa a matsayin yin nasarar gaskiya a kan karya.