Majalisar Wakilai ta fara kokarin yin amfani da karfin tuwo kan ikon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan sashe na 84(8) na Dokar Zabe ta Kasa da ke magana kan daliget na alfarma.
Yunkurin ya zo ne bayan Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Toby Okechukwu da dan majalisa Ben Ibakpa suka gabatar a zauren majalisar ranar Laraba.
- ‘Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ne ya hana ta ci gaba’
- Majalisar Dokokin Kano ta bai wa Ganduje damar karbo bashin N10bn
’Yan majalisar sun yi korafin cewa wasu daga cikin tanade-tanaden sassan dokar na da tarnaki kamar yadda aka gani yayin zabukan fitar da gwani da jam’iyyu suka kammala a kwanan nan.
A cewar Mataimakin Shugaban Marasa Rinjayen, dole ne majalisar ta kammala aikin da ta fara na samar dokar da za ta kawo sauyi ga ilahirin yadda ake gudanar da zabe a Najeriya.
Ya ce, “A zahirin gaskiya, akwai bukatar a cire duk wani sashen da ke da harshen damo a cikin dokar, saboda akwai bangarorin da babu banbanci a dokar 2010 da ta 2022.
“A yanayin da za a ce Shugabannin Majalisar Dattawa guda biyu za su sauya sheka saboda wasu rikice-rikicen cikin gida, gaskiya akwai matsala.
“Idan ma hakan na nufin yin amfani da karfin tuwo daga majalisar kan Shugaban Kasa a kana bin da ya rattaba wa hannu, ya kamata mu yi hakan,” inji shi.
A nasa bangaren, Ben Ibakpa ya ce an kira su daga mazabunsu daban-daban ana yi musu korafe-korafe a kan sassan dokar.
Sai dai bayan sun gama gabatar da kudurorin nasu, Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya tunatar da su cewa ko da yake wa’adin kwana 30 da majalisar ke da shi kafin Shugaban ya sa hannu a gyaran ya kare, har yanzu akwai ragowar matakan da ya kamata a bi kafin a kai ga daukar matakin.
Idan za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ce Shugaban majalisar ya zargi tsarin daliget na zaben fitar da gwani da cewa shi ne ummul-aba’isun da da yawa daga cikin ’yan majalisar suka gaza samun tikitin dawowa.