Hukumar tsaro ta DSS ta ce akwai wasu ’yan siyasa da ke kokarin hana rantsar da zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ta hanyar yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya.
A ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa ce aka shirya za a rantsar da sabon shugaban, inda zia karbi ragamar kasar daga shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari.
Sai dai a cewar Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwa da yammacin Laraba, wadanda hukumar take zargi na ta duba hanyoyi da dama, cikinsu har da kokarin samo umarnin kotun da zai hana rantsuwar ta yadda dole za a kafa gwamnatin rikon kwarya.
Afunanya ya kuma ce yanzu haka mutanen na shirye-shiryen daukar nauyin zanga-zanga a manyan biranen Najeriya ta yadda za a ayyana dokar ta-baci.
Sanarwar ta ce, “Hukumar na kallon irin wadannan yunkurin ba wai kawai a matsayin wanda bai dace ba, kazalika kuma yin zagon kasa ne ga Kundin Tsarin Mulki da kuma kokarin jefa kasa cikin rikicin ba gaira ba dalili.
“Wannan ba abu ba ne mai yuwuwa, koma yin karan tsaye ne ga tsarin Dimokuradiyya da kuma ra’ayin ’yan Najeriya masu son zaman lafiya,” in ji sanarwar.
DSS ta kuma ce tana goyon bayan shirye-shiryen mika mulki cikin ruwan sanyi, kuma za ta yi aiki tukuru wajen ganin hakan ta tabbata.
“A kan haka, muna aike wa da kakkarfan sakon gargadi ga irin wadannan mutanen da ke son yi wa Dimokuradiyya a Najeriya zagon kasa da su kuka da kansu kuma su canza shawara tun da wuri.
“Muna kuma kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da bangaren shari’a da kafafen yada labarai da kungiyoyin fararen hula da su yi taka-tsantsan wajen kauce wa yin amfani da su wajen kawo wa tsarin zaman lafiya cikas.
“Yayin da za mu ci gaba da sanya idanu, hukumar DSS ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sanya kafar wando daya ta hanyar daukar matakin doka a kan irin wadannan bata-garin ’yan siyasar marasa kishin kasa,” in ji sanarwar da DSS.