✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai taimakekeniya a tsakanin ma’aikatan BBC – Saleh Halliru

Dokta Saleh Halliru na daya daga cikin ’yan Najeriya da suka je birnin Landan da ke kasar Ingila da niyyar karo karatu amma suka samu…

Dokta Saleh Halliru na daya daga cikin ’yan Najeriya da suka je birnin Landan da ke kasar Ingila da niyyar karo karatu amma suka samu kansu a sashin Hausa na rediyon BBC, ya yi wa Aminiya bayanin yadda ya fara aiki a wurin da yadda ya bar wurin da kuma inda yake aiki a yanzu.

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Saleh Halliru: Sunana Saleh Halliru, an haife ni a wani gari da a ke kira Riruwai hedkwatar karamar Hukumar Dogowa a Jihar Kano. Yanzu shekaruna sun tasar wa 60. A garin Riruwai na fara karatun firamare a 1962, sai dai a 1966 na koma Kano inda na ci gaba da karatu a makarantar firamare ta Gwale, a can na karasa a 1969. Bayan nan sai na je makarantar sakandare ta Rano a 1970, na kammala a 1974, mu ne rukunin farko na daliban da suka kammala a makarantar.
Na je Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na samu digiri a Ilimin Kimiyyar Siyasa a 1978, bayan nan ne sai na yi aikin yi wa kasa hidima a Jihar Ogun. Daga nan sai na samu aiki a Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato a cibiyar adana bayanai na dakin karatun jami’ar, na yi aiki na tsawon wata shida, daga nan kuma sai suka tura ni kasar Amurka na yi shekara daya, inda na yi digiri na biyu, bayan nan na dawo jami’ar na ci gaba da aiki har na shekara shida.
To Daga nan ne sai na tafi Jami’ar Landan na yi digirin digirgir (PhD) a bangaren tsarin bayanai da adana bayanai, kuma na je can ne a 1987, kuma tun lokacin ne kuma na fara aiki da BBC a matsayin ma’aikaci na wucin-gadi, saboda shi karatun digirin digirgir ba darasi ba ne na shiga aji a koyaushe, ya fi karfi wajen nazarce-nazarce da rubuce-rubuce, to hakan ya ba ni sukunin fara aiki da BBC wanda kuma ya taimaka mini wajen karatuna da kuma kula da iyali, kasancewar na je can tare da ita, saboda a lokacin kudin da a ke bayarwa ga ma’aikata da ke karo ilimi ba zai gamsar ba. To, bayan na kammala karatun a shekarar 1991, ina shirin zan dawo gida, sai BBC suka ce ai dama suna bukatar karin ma’aikata, in zauna in yi musu aiki. To ka ji ta yadda na fara aiki da su. Na ci gaba da aiki a wajen har na tsawon shekara biyar zuwa shida.
Aminiya: Wannan ya nuna ke nan a BBC ne ka fara aikin jarida?
Saleh Halliru: kwarai kuwa a wajen ne na fara aikin jarida, BBC waje ne na hadin kai, ko da ba ka gane wani abu ba, za a taimaka maka har ka iya, kuma dama aikin namu ya shafi fassara labarai ne, idan wani abu ya kakare maka dama ga ’yan uwa, kana tambaya wani sai ya yi maka tuni, a gaskiya akwai hadin kai da taimakekeniya.
Aminiya: To dama kana da sha’awar aikin jarida ne ko dai zaman Landan ne ya sa ka shiga?
Saleh Halliru: A gaskiya zaman can ne ya ba ni karfin gwiwa, kasancewar ina bukatar kudi da zai tallafa mini ci gaba da zaman karatuna a can da kuma rike iyali a lokaci guda. To kuma ko da na fara wasa-wasa sai shugaban sashin Hausa na lokacin Barry Barges ya karfafa mini gwiwa, don a lokacin muna matsayin ma’aikata ne na wucin gadi, sai wata rana yake gaya mini cewa, “A tsarinmu ba ma barin ma’aikatan wucin gadi su yi aikin kwana saboda yana bukatar ka yi komai kai kadai, kana ganin idan na bar ka za ka iya rike wajen nan da dare kai kadai?” Sai na ce mai zai hana, shi ke nan kuma sai abun ya zama kamar jiki, har dai na zama cikakken ma’aikaci. To idan ka hada da aikin da na yi na wucin gadi da kuma na cikakken ma’aikaci, to, na shekara kamar goma ke nan a BBC, sai dai na sake komawa wajen bayan wasu shekaru uku inda na yi aikin shekara hudu, duka-duka dai na yi aiki da BBC shekara 14 ke nan. Ayyukan sun hada da gabatar da shirye-shiye da kuma tsara shirye-shiryen.
Aminiya: Kana iya tuna wadanda ka yi aiki da su?
Saleh Halliru: Mun yi aiki da Usman Muhammed da Umar Yusuf karaye da Jamila Tangaza da Bilkisu Labaran da Isa Abba Adamu da Yusuf Muhammad Kankiya da Babandi Abubakar Gumel da Mustafa Chinade da Ibrahim Usman Yakasai da ma wadanda suke wajen har yanzu irin su Mansur Liman da Alhadji Juli Kulbari da A’ishatu Musa da sauransu.
Aminiya: To daga can fa sai ina?
Saleh Halliru: To bayan na bar BBC a 1997 sai na samu aiki da gwamnatin kasar Singapore a ma’aikatarsu ta watsa labarai, na kuma shekara uku ina aiki a can. A shekarar 2000 sai na sake komawa BBC a lokacin Isa Abba Adamu ne ke shugabantar wajen, har zuwa shekara ta 2004.
Aminiya: To ga shi ka dawo gida Najeriya wane aiki kake yi a yanzu?
Saleh Halliru: Ina aiki ne a Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC) kuma kasancewar tun aikina na farko a bangaren na yi aiki, sai NCC ta turo ni wannan cibiyar koyarwa da ta bude mai suna Digital Bridge Institute. NCC ta bude wannan makaranta ne don cike gibin ilimin sadarwa da kasar nan ke da tsananin bukata, musamman bayan kakkafa kamfanonin sadarwa na wayan tafi-da-gidanka, sai ga shi babu kwararru da za su gudanar da harkar daga nan gida ta wajen kafa na’urorin da kuma gyara su. Muna koyar da ilimin sadarwa, muna koyar da kimiyyar sadarwa ta zamani (IT) da sauransu. Kamfanonin sadarwa irin su MTN da sassan kula da sadarwa na ma’aikatu da kamfanoni na turo ma’aikatansu muna ba su horo, a bangaren ilimin sadarwa, a madadin NCC. Na kuma zauna a bangarori da dama, na yi daraktan kasuwanci, na yi daraktan gudanarwa ko kula da ma’aikata, ga shi nan dai wurare da dama.
Aminiya: To yaya za ka kwatanta aikinka a nan gida da wanda ka yi a waje?
Saleh Halliru: Hakika akwai bambancin aiki a nan da kuma wanda na yi a waje, misali a nan akwai ka’idoji na gwamnati a tafiyar da aiki wadanda idan aka ce dole sai an bi su, za su jawo hana abubuwa sauri ko ma su mayar da su baya. To amma ka ga aikin da na yi a waje kamar na BBC babu irin wadannan matsaloli, idan za mu bukaci kashe kudi wajen yin aiki zai samu cikin hanzari ba tare da abu ya tsaya ba. Kuma aikin da na yi a can aiki ne na karba-karba, wani zubin kana ofis da dare, wani zubin da rana, nan kuwa daga Litinin har zuwa Juma’a zan fito daga gida tun takwas ina ofis har zuwa karfe biyar. Sannan idan ka duba na BBC kuma, bai da rana bai da takamanmen lokaci, wani lokaci za ka je aiki da dare wani lokaci da safe, kuma ya hada har da ranakun karshen mako, amma idan ka zo wajen aikin za ka fuskanci aikin, sannan kuma ran da ba ka zo ba za ka huta a gida ko ka yi wani abu daban.
Aminya: Yaya batun iyali?
Saleh Halliru: Eh, dama tun lokacin da na tafi BBC da iyalina na je, kuma muna tare da ’ya’ya a yanzu haka duk sun girma gwargwado, akwai wadanda sun daura a kan shekara talatin.