✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai sauran matsala kan mafi karancin albashi

Ga dukan alamu, har yanzu akwai sauran rina a kaba, dangane da batun mafikaracin albashi a Najeriya, duk  da cewa Majalisar Kasa ta amince a…

Ga dukan alamu, har yanzu akwai sauran rina a kaba, dangane da batun mafikaracin albashi a Najeriya, duk  da cewa Majalisar Kasa ta amince a biya Naira dubu 30 ga ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da kuma Naira dubu 27 ga jihohi, a matsayin mafi karancin albashi.

A ranar Talatar da ta gabata ce dai Majalisar Kasa ta zauna, a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ta cimma wannan matsaya. Kafin a cimma wannan matsaya, an yi ta kai-ruwa-rana a tsakanin Kungiyar Kwadago da Gwamnatin Tarayya, al’amarin da a kwanakin baya ya kai ga kungiyar ta shiga zanga-zangar lumana domin jawo hankalin gwamnati ga karin albashin.

Bayan kammala zaman na Majalisar Kasa, Ministan Kwadago, Chris Ngige ya gana da manema labarai, inda ya ce a ranar za a tura wa Majalisar Dokoki ta Kasa da batun domin zartar da shi ya zama doka. Sai dai kuma a hannu daya, Kungiyar Kwadago t aKasa  ta ce matukar ba a kai wa majalisar kudirin domin zartarwa ba, to za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a mako mai zuwa.

Ngige ya kara haske dangane da mafi karancin albashin da aka amince da shi. Ya ce duk wata ma’aikata mai dauke da ma’aikata 25, za ta biya Naira dubu 27 mafi karanci, sai dai tana iya karawa sama da wannan adadi idan ta so amma ba dai ta rage ba. Ya ce Majalisar Kasa ta amince da wannan tsarin albashi. “Majalisar Zartarwa ta amince Shugaban Kasa ya aike wa Majalisar Dokoki ta Kasa kudirin dokar sabon tsarin albashin da aka amince da shi,” inji shi.

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC)  ta yi watsi da batun Naira dubu 27 a matsayin mafi karancin albashi da Majalisar Kasa ta amince da shi ga jihohi a Talatar da ta gabata. Dokta Peter Ozo-Eson, Babban-Sakataren Kungiyar Kwadago ya bayyana cewa Majalisar Kasa ba ta da hurumin zartar da wani adadin albashi na daban da wanda kwamitoci uku suka yanke a kwanakin baya kuma har suka bayyana rahotonsu a kan haka.

“Bai dace ba, kuma karamar magana ce daga Gwamnatin Tarayya da take ta jawo tsaiko wajen mika kudirin doka dangane da sabon tsarin albashi mafi karanci ga Majalisar Dokoki ta Kasa ta hanyar zaben Naira dubu 27 mafi karanci da Majalisar Kasa ta yi, ” inji shi.

Sakataren ya ce, a yau Jumu’a ce shugabannin kungiyar za su zauna domin tattaunawa dangane da wannan batu da Majalisar Kasa ta yanke kan batun albashi mafi karanci. Ya ce bayan sun kammala taron na yau, kada a sake a zargi kungiyar tasu, kan irin matakin da za ta dauka a kan Gwamnatin Tarayya, wanda yana iya haddasa tsaiko ga harkokin tattalin arzikin kasa.