Malam Tanimu wani tsohon mai sayar da jarida ne a Kudancin Kaduna da ya samu rufin asiri a cikin harkar. Ya bayyana wa wakilinmu irin alherin da matsalolin da harkar sayar da jarida ke ciki musamman a wannan zamani na karanta labarai ta hanyar Intanet.
Aminiya: Za mu so ka fara gabatar mana da kanka?
Tanimu: Sunana Tanimu Muhammad Madaki. Yanzu ina da kimanin shekara 58 a duniya.
Aminiya: Mece ce sana’arka?
Sana’ata tallan jarida wadda na fara sayarwa tun a shekarar 1987.
Aminiya: Ko za ka iya tuna wasu daga cikin sunayen jaridun da kake sayarwa a da wadanda yanzu babu su?
Ba dai duka ba saboda wasu jaridun an dade da daina buga su, kuma na manta wasu, amma daga cikin na turanci akwai jaridar New Nigerian da Daily Times, da kuma Sketch. Cikin na Hausa kuma akwai irinsu Gaskiya Ta fi Kwabo, Amana, Alkalami, Zuma, Rana da kuma Hantsi.
Aminiya: Wacce irin riba ko nasara ka samu a harkar sayar da jarida?
Akwai nasarori kam da yawa da na samu domin a harkar sayar da jarida. Da farko dai za ka san manyan mutane sannan idan mutum ya rike gaskiya akwai rufin asiri sosai a sayar da jarida.
Aminiya: Yaya batun iyali fa?
A yanzu haka dai ina da ’ya’ya takwas wadanda suke da rai.
Aminiya: Yaya batun karatunsu, dukkansu ta hanyar sayar da jarida kake daukan nauyinsu?
Dukkaninsu ta hanyar sayar da jarida nake ciyar da su, na tufatar da su sannan na biya musu kudin makaranta, Alhamdulillahi.
Aminiya: Wadanne matsaloli ko kalubale kuke fuskanta yanzu a harkar sayar da jarida?
Da farko dai jaridun sun yi kudi yanzu ba kamar da ba. Sannan yanzu kuma mutane sun fi karanta jaridu ta hanyar Intanet ko a wayoyinsu na sadarwa kuma gaskiya ni ina ganin laifin kamfanonin jaridun ne domin su suke turawa da zaran mutum ya biya take zai gama karantawa wani karfe daya na dare ya gama karantawa wani kuma gari na wayewa zai bude waya ya karanta, to da zaran ka kai wa mutum tallanr jarida da safe, sai ya ce ai ya gama karanta labaran. Duk da dai su kamfanonin jaridun ba su da asara tun da suna samun tallace-tallace, sai dai mu masu sayarwa ne kawai ya shafi sana’armu.
Aminiya: To mece ce shawarar da za ka ba irin wadannan mutane, wato akwai wani bambanci ne wajen karanta labarai a wayoyi da kuma sayen jaridu?
kwarai kuwa, ai shi karanta jarida ya fi domin shi ne babban shaida. Yanzu ko da gardama ce ta hada ka da wani mutum kan wani labari da ka gani idan ya ce bai yarda ba, za ka iya dauko jaridar ka nuna masa tun da akwai rana da kwanan wata ko da kuwa labarin ya shekara 30 ne, wanda ka ga a waya ba haka ba ne. Idan labari ya wuce shike nan,ita ko jarida akwai wadanda suke ijiye ta tsawon shekaru ko don saboda tarihi ko don wani labari don haka ina ba da shawara a ci gaba da sayen jarida.
Aminiya: A karshe wacce shawara zaka ba matasa masu zaman banza kan su daina raina sana’a komai kankantarta su tashi su rungumeta?
Shawarar da zan ba matasa ita ce su tashi su kare mutuncinsu. Yanzu kamar yawon sayar da jaridar nan da nake yi wasu suna ganin kamar wahala nake yi, amma ina kare mutuncina ne tunda yafi zaman banza, ko yawon banza da zuwa maula ko fadanci kana rokon mutane. Zaman banza baida kyau wallahi ko yaya mutum ya rike sana’a da gaskiya to idan Allah Ya yarda Allah zai taimake shi ya rufa masa asiri komai kankantarta kuwa.