Wani likitan kwakwalwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH)da ke Zariya, Farfesa Taiwo Lateef Sheikh, ya ce akwai masu fama da matsalar kwakwalwa kusan miliyan 70 a Najeriya.
Sai dai ya koka kan karancin likitocin kula da kwakwalwar a Najeriya, inda ya ce su 300 ne kacal ke duba mutum sama da miliyan 200 da ke kasar nan.
- Yadda mutane suka yi tara-tara wajen kama wata mai yunkurin satar dalibi a Kano
- 2023: Zawarcin Kwankwaso da APC ke yi ya tayar da kura
Likitan, wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawarsa da wakilinmu a Zariya ranar Juma’a, ya ce lamarin abin takaici ne kuma yana bukatar daukin gaggawa daga gwamnati.
Kwararren likitan ya yi korafin cewa akwai gogaggun likitocin kwakwalwa ’yan asalin Najeriya sama da 2,000 da ke aiki a Amurka da kasashen Turai.
A cewarsa, “Yanzu haka, akwai kwararrun likitocin kwakwalwa kimanin 3,000 wadanda aka haifa suka girma kuma suka yi karatu a Najeriya da ke aiki a kasashen duniya daban-daban.”
Ya ce kididdiga na nuni da cewa a Najeriya, adadin likitan kwalkwalwa ga yawan jama’ar duniya shi ne likita daya ga duk mutum miliyan daya.
Farfesa Taiwo ya lura cewa alkaluma sun nuna cewa a fadin duniya, a cikin kowanne mutum uku, daya daga cikinsu na fama da matsalar kwakwalwa.
Sai dai masanin ya ce a Najeriya, adadin ya zarta haka, inda ya ce akwai masu matsalar kwakwalwa tsakanin miliyan 50 zuwa miliyan 70.
Likitan ya ce wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa matsalar kwakwalwar ba suna nufin mutane na da tabin hankali ba ne, sai dai matsaloli irinsu gajiya, matsananciyar damuwa ko yawan tunani ne ke kawo su.