Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce, akwai wasu masu fada aji da ke kokarin ganin an halasta tabar wiwi a Najeriya.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ne ya bayyana haka ne a wajen wani taro da halarta ranar Alhamis a Legas.
- ’Yan Najeriya miliyan 133 na fama da talauci —Rahoto
- ’Yan sanda sun kama mijin da ya azabtar da matarsa da yunwa
Ya ce, “Wasu jiga-jigan Najeriya sun ba da himma wajen neman a halasta tabar wiwi domin ba su damar noma ta.
“Wannan kuwa wata alama ce ta daure wa matasan kasar gindi wajen ci gaba da aikata ba daidai ba,” inji shi.
A cewarsa, maimakon neman a halasta wiwi a kasa, “kamata ya yi jama’a su goya mana baya wajen yaki da ta’ammali da ita.”
Kazalika, ya ce masu safarar miyagun kwayoyi kimanin su 19,000 ne suka fada a komar NDLEA a tsakanin shekaru biyun da suka gabata.
Kazalika, ya ce an samu nasarar hukunta mutum 3,011 daga cikin adadin da aka kama.